Bacewar yaro: Kotu ta yanke wa fasto hukuncin daurin rai da rai

Bacewar yaro: Kotu ta yanke wa fasto hukuncin daurin rai da rai

- Kotu ta yanke wa fasto hukuncin daurin rai da rai a jihar Ondo kan bacewar wani karamin yaro

- Tun a watan Nuwamban 2019 ne wani yaro mai suna Gold Kayode ya bata a cocin bayan iyayensa sun ajiye shi a sashin yara

- Kotun ta samu faston da wasu mutum bakwai da laifin garkuwa da taimakawa wurin yin garkuwa

DUBA WANNAN: Kishi ya saka ango ya kashe amaryarsa da duka a wurin bikin aurensu a Rasha

Batar yaro: Kotu ta yanke wa fasto hukunin daurin rai da rai
Batar yaro: Kotu ta yanke wa fasto hukunin daurin rai da rai. Hoto:@MobilePunch
Asali: Twitter

Babban kotun jihar Ondo ta yanke wa wanda ya kafa cocin Sotitobire Praising Chapel, Fasto Samuel Babatude da aka fi sani da Alfa Babatunde hukuncin daurin rai da rai kan bacewar wani yaro mai shekara daya, Gold Kolawole, a cocinsa.

An sace yaron ne a watan Nuwamban 2019 a yayin da suka zo cocin kuma aka tura shi sashin ibada na kanana yara a Sotitobire Praising Chapel da ke Oshinle Quarters Akure kuma har yanzu ba a gan shi ba.

KU KARANTA: Ka yi amfani da ICT don yakar 'yan ta'adda da 'yan bindiga - Tambuwal ga Buhari

Hakan yasa aka kama faston da wasu mambobin cocin su bakwai aka gurfanar da su a kotun majistare kan tuhumar aikata laifuka guda shida.

Daga bisani aka mayar da shari'a zuwa babban kotun jihar.

Da ya ke yanke hukunci a ranar Talata, Mai shari'a Olusegun Odusola ya samu wadanda ake tuhumar da laifuka biyu na garkuwa da kuma taimakawa wurin garkuwar bisa hujojjin da masu shigar da karar suka gabatarwa kotu.

A wani labarin, 'Yan bindiga sun kashe jami'in hukumar yaki da masu fasakwabri wato kwastam yayin da ya ke bakin aikinsa a kauyen Dan Arau da ke babban titin Katsina/Jibya.

Sun kashe Garba Nasiru, mai mukamin mataimakin sufritanda ne yayin wani hari mai ban mamaki da suka kai a ranar Juma'a sannan suka tafi da bindigarsa AK 47.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel