Takarar WTO: Kungiyar EU ta na tare da Ngozi Okonjo-Iweala da Myung-Hee

Takarar WTO: Kungiyar EU ta na tare da Ngozi Okonjo-Iweala da Myung-Hee

- Ngozi Okonjo-Iweala za ta iya zuwa mataki na gaba a takarar kungiyar WTO

- A makon nan ake sa ran za a fito da sabon shugaban da zai rike WTO a Duniya

- Tsohuwar Ministar tattalin Najeriya, Okonjo-Iweala, ta na cikin masu takarar

Rahotanni daga jaridar Bloomberg sun bayyana cewa kungiyar kasashen Turai watau EU, ta marawa Ngozi Okonjo-Iweala a takarar WTO.

EU ta ba tsohuwar Ministar tattalin arzikin Najeriya watau Ngozi Okonjo-Iweala, kwarin gwiwa a takarar shugabancin kungiyar WTO da za ayi.

Haka zalika kungiyar ta Turai ta na tare da abokiyar takarar ‘Yar Najeriyar, Yoo Myung-hee, wanda ta fito daga kasar Koriya a nahiyar Asiya.

KU KARANTA: Kasar Masar ta na yi wa Okonjo-Iweala a WTO

A ranar Litinin, 5 ga watan Oktoba, 2020, wata majiya ta shaidawa jaridar wajen cewa manyan kungiyar sun kai ga daukar wannan mataki.

A tsakiyar makon nan da ake ciki za a fitar da sunayen ‘yan takarar da zasu isa zuwa matakin karshe, inda za a fito da sabon shugaban WTO.

Kwanakin baya aka fara shirin zaben wanda zai shugabanci kungyiyar WTO, wadanda su ka fara shiga takarar sun hada da mata uku da maza biyar.

Daga baya an zaftare wasu mutum uku aka bar mutane byar; Okonko-Iweala, Yoo Myung-hee, Amina Mohamed, Maziad Al-Tuwaijri da Liam Foxx.

KU KARANTA: Kungiya ta yi na'am da takarar Okonjo-Iweala a WTO

Takarar WTO: Kungiyar EU ta na tare da Ngozi Okonjo-Iweala da Myung-Hee
Ngozi Okonjo-Iweala Hoto: Twtter/NOIweala
Asali: Twitter

Idan rahotannin sun tabbata, kungiyar Turan ta yi watsi da Liam Foxx na kasar Birtaniya, ta zabi ta goyi bayan mutumiyar Najeriyar ko Myung-Hee.

Kafin nan Okonjo-Iweala ta samu goyon bayan kungiyar ECOWAS ta kasashen yammacin Afrika.

Tun kwanakin baya ku ka ji cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya zabi Okonjo-Iweala domin ta rike mukamin shugabar WTO ta Duniya.

A dalilin haka ne Buhari ya janye takarar Yonov Fredrick Agah mai wakiltar Najeriya a WTO.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel