Shugaban JIBWIS, Lau ya tabbatar da rasuwar Malam Ibrahim Damaturu

Shugaban JIBWIS, Lau ya tabbatar da rasuwar Malam Ibrahim Damaturu

- Jihar Yobe ta rasa ‘Ya ‘yanta biyu a cikin kusan lokaci guda. Daga ciki har Shehin Malamin nan, Ibrahim Damaturu ya rasu ranar Lahadi

- Honarabul Sabo Garbu shi ma ya rasu, za a birne shi an jima. Gwamna Mai Mala Buni ya yi jawabi game da wadannan rashin da aka yi

Labari maras dadi ya zo mana cewa wani shehin malami da ake ji da shi a jihar Yobe, Malam Ibrahim Damaturu ya rasu a cikin makon nan.

Shugaban kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a wa Iqamatus Sunnah watau JIBIWS, Abdullahi Bala Lau, ya tabbatar mana da wannan rasuwa a jiya.

Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi magana a shafin Twitter a ranar Litinin, 5 ga watan Oktoba, 2020.

KU KARANTA: Shugaban Izala ya karyata rade-radin cewa ya mutu

Da ya ke magana da kimanin karfe 1:30 na rana, Sheikh Bala Lau ya ce shugaban majalisar malaman kungiyar JIBWIS na jihar Yobe ya cika.

Sheikh Lau ya fara jawabi ne da rubuta: INNALILLAHI WA INNAA'ILAIHIRAJI'UN; Ma’ana daa Allah (SWT) mu ke, kuma gare Sa za mu koma.

"Mun samu labari mai tada hankali na cikawar shugaban majalisar malamai na jihar Yobe, Malam Ibrahim Damaturu." Inji Bala Lau a shafin na sa.

Shugaban na kungiyar JIBWIS, ya yi wa marigayin addu’ar samun Aljannah. Ya ce: “Allah ya gafarta kura-kuransa, ya ba shi gidan Aljannah. Ameen.”

Shugaban JIBWIS, Lau ya tabbatar da rasuwar Malam Ibrahim Damaturu
Jama'a wajen jana'izar Ibrahim Damaturu Hoto: Facebook/JIBWIS Damaturu
Asali: Facebook

KU KARANTA: Da gaske JIBWIS ta samu kudi daga Gwamnatin Zamfara?

Haka zalika gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya girgiza da mutuwar wannan Bawan Allah da kuma Honarabul Sabo Garbu, Dan Madamin Fika.

Shi ma Sabo Garbu ya rasu ne a lokaci guda da wannan malami da ya yada ilmi ga yara da manya. Shi kuma Garbu, ‘dan siyasa ne mai taimakon al’umma.

Ku na da masaniya cewa maganar bude Jami'ar addini ta yi nisa, kungiyar Jama’atul Izatil Bidi’a wa Iqamatun Sunnah ta Najeriya za ta gina jami’a a Jigawa.

Kwamitin tsare-tsare da gudanarwa na kungiyar ya kammala aikinsa, har an fara daura gini.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng