Mun warware matsalar jam'iyyar APC a jihohi 11 - Mai Mala Buni

Mun warware matsalar jam'iyyar APC a jihohi 11 - Mai Mala Buni

- Jam'iyyar APC mai mulki ta dade ta na fama da rigingimun cikin gida a tarayya da jihohi da dama

- Rikicin shugabanci ya yi sanadiyar dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomhole

- APC ta nada Mai Mala Buni; gwamnan jihar Yobe, a matsayin shugaban kwamitin riko na jam'iyya bayan dakatar da Oshiomhole

Jam'iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa ta warware manyan matsaloli a wasu jihohi 11 da ke fama da rikici.

Shugaban rikon kwarya na jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, ne ya sanar da hakan a wurin taron rantsar da kwamitin sulhu a Abuja.

A ranar Talata ne Buni ya rantsar da kwamitin sulhu da yakin neman zabe a sanatoriyar jihar Bayelsa ta tsakiya da ta yamma.

Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Mohammed Inuwa Yahaya, ne zai jagoranci kwamitin da Buni ya rantsar.

DUBA WANNAN: Sunday Dare: Sabon shirin gwamnatin Buhari na samawa matasa 1,000,000 aiki a Nigeria

Duk da bai ambaci sunan jihohin ba, Buni ya bayyana cewa sun samu nasarar dawo da manyan 'yan APC cikin jam'iyyar saboda sulhun da su ke yi.

Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Sanata Ovie Omo-Agege, shine mataimakin shugaban kwamitin yayin da Barista Ekemini Cletus Udoh aka bashi mukamin sakatare.

Mun warware matsalar jam'yyar APC a jihohi 11 - Mai Mala Buni
Mai Mala Buni da manyan APC a jihar Ondo
Asali: Twitter

A ranar Litinin ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa tsohon mataimakin Shugaban-ƙasa, Atiku Abukar, ya magantu a kan bayyanar wasu fastocin yaƙin neman zaɓensa da suka mamaye yanar-gizo tun satin da ya gabata.

DUBA WANNAN: Sai Murna: Buhari ya amince a bawa daliban da suka yi karatun NCE aiki, ya kara shekarun aikin malamai

A cikin wani jawabi da ya fito ranar Litinin, Atiku, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2019, ya nesanta kansa daga bullar fastocin.

A jikin fastocin, an gabatar da Atiku a matsayin mutum na kwarai da zai iya ceton Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar, a yayin da yake maida martani a kan batun, ya ce hankalinsa yafi karkata wajen ganin jam'iyyarsa ta PDP ta samu nasarar lashe zaɓen jihar Ondo.

Martanin ya fito ne ta hannun mai yaɗa labaran Atiku, Paul Ibe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel