Babbar magana: Ana shirin zaben Ondo, PDP ta samu goyon bayan wasu jam'iyyu 11

Babbar magana: Ana shirin zaben Ondo, PDP ta samu goyon bayan wasu jam'iyyu 11

- Yunkurin Eyitayo Jegede na sake neman kujerar gwamnan jihar Edo a karo na biyu na samun gagarumin goyon baya

- Kimanin jam’iyyun siyasa goma sha daya ne suka hade da PDP domin kalubalantar tazarcen Gwamna Rotimi Akeredolu

- Za’a yi zaben gwamnan Ondo a ranar Asabar, 10 ga watan Oktoba, inda mataimakin gwamna Agboola Ajayi ma zai gwada sa’arsa

Gabannin zaben gwamnan Ondo, kimanin jam’iyyun siyasa goma sha daya ne suka hade da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), wanda hakan ya kara wa takarar Eyitayo Jegede (SAN) karfi.

Shugaban jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Oladele Ogunbameru, wanda kuma shine kakakin jam’iyyun siyasan ne ya sanar da hakan a ranar Litinin, 5 ga watan Oktoba, a Akure, babbar birnin jihar.

Hukumar zabe ta kasa ma zaman kanta, ta sanya ranar Asabar, 10 ga watan Oktoba, domin gudanar da zaben gwamnan jihar Ondo.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Buhari ya amince a ƙarawa malamai albashi da shekarun aiki

Babbar magana: Ana shirin zaben Ondo, PDP ta samu goyon bayan wasu jam'iyyu 11
Babbar magana: Ana shirin zaben Ondo, PDP ta samu goyon bayan wasu jam'iyyu 11 Hoto: @AIT_Online
Asali: Twitter

Gwamna Rotimi Akeredolu na fuskantar babban kalubale a lamarin tazarcensa domin zai gwabza ne da Jegede wanda yake tsohon atoni janar kuma kwamishinan shari’a na jihar.

Wani babban abokin hamayya kuma shine Agboola Alfred Ajayi, mataimakin gwamnan Ondo, wanda ke neman takararsa a jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP).

Da yake zantawa da manema labarai yayin sanar da hadewar, Shugaban SDP, ya ce jam’iyyun siyasan sun hade ne domin yakar mummunan shugabanci na Akeredolu.

Ogunbameru ya ci gaba da bayyana cewa hadewarsu wani kokari ne na ceto jihar Ondo daga tabarbarewa a karkashin gwamnati mai mulki.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Buhari ya amince da fitar da biliyan 10 domin kidaya

A gefe guda, Uche Secondus, shugaban PDP ya shawarci Gwamna Godwin Obaseki na Edo da ya zauna lafiya da abokan hamayya a jihar wadanda ke da muradin aiki tare da shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel