Yan kwanaki kafin zaben gwamnan Ondo: An yi harbe-harbe a garin Akure
- An yi harbe-harbe a Akure, babbar birnin Ondo yan kwanaki kafin zaben gwamnan jihar
- An tattaro cewa yan bangar siyasa ne suka fafata a tsakaninsu
- Mutane da dama sun jikkata a artabun da aka yi tsakanin magoya bayan PDP da APC
Gabannin zaben gwamnan jihar Ondo, wasu yan bangar siyasa sun yi artabu a tsakaninsu inda suka yi harbe-harbe a yankin Akure, babbar birnin jihar.
An tattaro cewa lamarin ya yi sanadiyar jikkata mutane uku, inda suka ji munnan raunuka sakamakon harbin bindiga, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.
Mutane da dama sun ji rauni yayin da magoya bayan manyan jam'iyyun siyasa biyu masu adawa na All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP), suka yi arangama a cikin garin.
KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Buhari ya amince a ƙarawa malamai albashi da shekarun aiki
A gefe guda kuma, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), ta yi jawabi ga taron manema labarai a ranar Litinin, 5 ga watan Oktoba, a Akure gabanin zaben gwamnan na jihar Ondo.
Za a dai gudanar da zaben gwamnan ne a ranar Asabar, 10 ga Oktoba 10, tare da jam’iyyun siyasa 17 da za su fafatawa.
Manyan ‘yan takarar sun hada da Gwamna Rotimi Akeredolu na APC da Eyitayo Jegede na PDP da kuma Agboola Ajayi, mataimakin gwamna mai ci wanda ke takara a karkashin jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP).
KU KARANTA KUMA: Babbar magana: Sule Lamido ya caccaki Osinbajo, Zulum da sauransu kan hasashen ɓallewar Nigeria
A wani labarin kuma, Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi martani a kan yawan rikici da ake ta samu yayinda ake shirye-shiryen zaben gwamnan Ondo.
Babbar jam’iyyar adawar ta yi ikirarin cewa jam’ iyyar APC na aiki tare da Gwamna Rotimi Akeredolu domin razana dan takararta, Jegede Eyitayo da mutanen jihar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng