Ku maye gibin kujerun yan majalisar APC jihar Edo - PDP ga INEC
- Bayan nasara a zabe, jam'iyyar PDP ta ki rantsar da yan majalisan APC
- Tun bayan zaben shekarar 2019, yan majalisar APC 14 sun kauracewa majalisa saboda zaben kakakin tumun daren da akayi
Shugaban PDP reshen jihar Edo, Tony Azegbiemi, yayi kira ga hukumar zabe ta kasa, INEC da ta gudanar da zabe wacce zata maya gibin kujeru 14 na majalissar, wacce shugaban majalissar jihar, Frank Okiye ya tabbatar da gibinsu a watan Disamban 2019.
Azegbiemi, a wata tattaunawa da gidan talabijin a garin Benin ranar Lahadi, yace jamiyyar zata rubatawa INEC wasika akan ta gudanar da zaben maye gurbin kujerun, cewar an hana mutane daga mazabun damar musharaka a majalissar jihar.
Yace, "Mun shiga damuwa saboda miliyoyin mutane sun rasa muryarsu a majalissar...Kuma muna so su samu wakilci. Zamu rubutawa INEC wasika domin ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na wajen gudanar da zabe akan wadannan mazabu 14."
KU KARANTA: Shugaban JIBWIS, Lau ya tabbatar da rasuwar Malam Ibrahim Damaturu
DUBA NAN: An sallami Donald Trump daga asibiti inda yake jinyar cutar Korona
Duk kokarin da akayi na magana da shugaban Victor Edoror yaci tura.
Amma hadimin daya daga cikin mambobin, wanda yayi magana cikin wani yanayi, yace, "Ba zaku maye gurbin kujerar da a cike take ba. Wannan al'amarin ya riga ya shiga hannun kotu."
A wani labarin, Uche Secondus, shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya shawarci Gwamna Godwin Obaseki na Edo da ya zauna lafiya da abokan hamayya a jihar wadanda ke da muradin aiki tare da shi.
Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Secondus ya bayar da shawarar ne a lokacin da ya jagoranci masu ruwa da tsaki na PDP a Edo domin mika godiya a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja, a ranar Litinin, 5 ga watan Oktoba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter:https://facebook.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng