Sabon hari: 'Yan bindiga sun halaka rayuka 9, sun raunata wasu tare da sace wasu a Katsina

Sabon hari: 'Yan bindiga sun halaka rayuka 9, sun raunata wasu tare da sace wasu a Katsina

- Wasu 'yan bindiga da ake zargin Fulani ne sun kai hari kauyuka biyu a karamar hukumar Batsari

- 'Yan bindigar sun halaka rayuka a kalla tara, sun sace wasu tare da raunata wasu masu tarin yawa

- A watanni kalilan da suka gabata ne wasu gagaruman 'yan bindiga suka kai harin daukar fansa kauyukan

'Yan bindiga da ake zargin Fulani ne sun kai hari wasu yankuna biyu da ke karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Kamar yadda Katsina Post ta wallafa, yankunan da aka kai harin sune Tsauwa da Gandu.

Jaridar ta wallafa cewa, a kalla rayuka tara suka salwanta yayin da wasu da yawa suka samu miyagun raunika kuma aka yi garkuwa da wasu.

KU KARANTA: Kano: Hotunan jami'an Hisbah suna yi wa matasa aski a tituna

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kashe rayuka 9, sun raunata wasu tare da sace wasu a Katsina
Sabon hari: 'Yan bindiga sun kashe rayuka 9, sun raunata wasu tare da sace wasu a Katsina. Hoto daga @SaharaReporters
Asali: Twitter

Idan za mu tuna, a watanni kadan da suka gabata ne 'yan bindiga suka kai harin daukar fansa a kauyen Tsauwa.

Kashe-kashe da garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a jihar Katsina duk da jami'an tsaron da suka yawaita a jihar.

KU KARANTA: Da duminsa: IGP Adamu ya haramta wa jami'an SARS wasu jerin ayyuka

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro ta ce dakarun sojin saman Operation Lafiya Dole ta samu babban nasara ta hanyar halaka tushe da maboyar 'yan ta'adda a yankin arewa maso gabas a ranar bikin zagayowar cikar Najeriya shekaru 60 da samun 'yancin kai.

Shugaban fannin yada labarai na rundunar, John Enenche, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Manjo Janar Enenche, ya ce a ranar 1 ga watan Oktoba, dakarun sojin sun kashe 'yan ta'adda masu tarin yawa da maboyarsu a Maima da Tusuy kusa da Warshale da Tongule a yankin Dikwa-Rann da ke Borno.

Ya ce nasarar an sameta ne bayan bayanan sirri da suka samu wanda ya bayyana inda 'yan ta'addan suke kuma suke samun mafaka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel