Hotunan hamshakan Sarakuna 6 na Afrika masu matukar arziki a karni na 21

Hotunan hamshakan Sarakuna 6 na Afrika masu matukar arziki a karni na 21

- Afrika tana da arzikin hamshakan masu sarauta masu tarin dukiya

- Da yawansu dukiyar ta samu ne sakamakon kasuwancin da suka fada

- Sarakunan da yawa sun mallaki dukiyoyi da suka kai miliyoyi zuwa biliyoyi

Baya ga Afirika na amfani da dokoki da siyasa wurin jagoranci, nahiyar na bada muhimmanci akan sarautar gargajiya.

Sarautar gargajiya na da matukar tasiri a Afirika.

Masu sarautar gargajiya na samun kudade daga mutanen yankunan da suke shugabanta, sayar da filaye da sauran su.

Baya ga haka, sarakunan gargajiya na da neman na kansu, wasunsu manyan 'yan kasuwa ne. Suna da iko sosai a masarautunsu har da alfarma a waje.

Suna kuma samun damar damawa a harkokin arziki daga hannun manyan masu hannu da shuni.

Anan akwai manyan sarakuna masu hannu da shuni a nahiyar Afirika a shekarar 2020.

Sarki Mohammed VI, dake kasar Morocco wanda yake da dala biliyan 5.4.

Sarki Mohammed VI shine sarki na 27 a masarautar Alaouite wanda ya gaji sarautar a watan Yuli 1999.

Mohammed VI ne sarkin da yafi kowanne sarki dukiya a Afirika, wanda yake juya kamfanin Societe Nationale d'Investissement dake kasar Morocco. An kimanta abubuwan da ya mallaka zasu kai dala Biliyan 10.

Sarkin yana juya harkokin arziki da kuma bunkasa harkar kasuwancin dake kara wa Morocco daraja a idon duniya.

Hotunan hamshakan Sarakuna 6 na Afrika masu matukar arziki a karni na 21
Hotunan hamshakan Sarakuna 6 na Afrika masu matukar arziki a karni na 21. Hoto daga Pulse.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Bakar ranar ga Boko Haram: Dakarun soji sun ragargaza maboya da wasu 'yan ta'adda a Borno

Fredrick Oba Obateru Akinrutan, Nigeria

Basaraken ya mallaki kudin da ya kai dala miliyan 300. Oba Obateru Akinrutan shine sarkin wani yanki na jihar Edo, yankin da ke da arzikin man fetur. Ya hau karagar mulkin a shekarar 2009.

Oba Obateru Akinrutan shine shugaban daya daga cikin manyan kamfanonin mai a Najeriya mai suna Obat Oil.

Hotunan hamshakan Sarakuna 6 na Afrika masu matukar arziki a karni na 21
Hotunan hamshakan Sarakuna 6 na Afrika masu matukar arziki a karni na 21. Hoto daga Pulse.ng
Asali: UGC

Oba Adeyeye Ogunwusi Eniitan, Nigeria

Ya mallaki dukiyar da ta kai dala miliyan 70. Oba Adeyeye shine sarkin Ooni na masarautar Ile-Ife. Ya hau karagar mulki a 2005.

Bayan sarautarsa, dan kasuwa ne hamshakin wanda ke harkar dillanci kuma shine shugaban majalisar zartarwa ta jami'ar Najeriya da ke Nsukka.

Hotunan hamshakan Sarakuna 6 na Afrika masu matukar arziki a karni na 21
Hotunan hamshakan Sarakuna 6 na Afrika masu matukar arziki a karni na 21. Hoto daga Pulse.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Kano: Uwa ta yi wa 'ya'yanta yankan rago saboda kishiya

King Mswati III, Swaziland

Yana da arzikin da ya kai a kalla dala miliyan 50. Ya hau karagar mulkin a watan Afirilun 1986 kuma ya hau a lokacin da yake da shekaru 18 a duniya.

Shi ke kuma da Tibiyo TakaNgwane, kamfanin da yake da dala miliyan 140 kuma jama'arsa sun matukar yadda da shi.

Hotunan hamshakan Sarakuna 6 na Afrika masu matukar arziki a karni na 21
Hotunan hamshakan Sarakuna 6 na Afrika masu matukar arziki a karni na 21. Hoto daga Pulse.ng
Asali: UGC

King Goodwill Zwelithini Kabhekuzulu, South Africa

Yana da arzikin da ya kai dala miliyan 19. Basaraken shine sarkin Zulu, kabilar da ta kasance mafi girma a kasar Afrika ta Kudu. Yana samun alawus dala miliyan 6 domin kula da gidan sarautar.

Hotunan hamshakan Sarakuna 6 na Afrika masu matukar arziki a karni na 21
Hotunan hamshakan Sarakuna 6 na Afrika masu matukar arziki a karni na 21. Hoto daga Pulse.ng
Asali: UGC

Otumfuo Osei Tutu II, Ashanti, Ghana

Ya mallaki dukiya a kalla dala miliyan 14. Otumfuso Osie Tutu II shine sarki na 16 na masarautar Ashanti da ke Ghana. Ya hau karagar mulkin a 1999 kuma ya kasance shugaban siyasar jama'ar Asante.

Hotunan hamshakan Sarakuna 6 na Afrika masu matukar arziki a karni na 21
Hotunan hamshakan Sarakuna 6 na Afrika masu matukar arziki a karni na 21. Hoto daga Pulse.ng
Asali: UGC

A wani labari na daban, Dino Melaye, tsohon sanata da ya taba wakiltar yankin Kogi na yamma, ya darzo sabuwar motar kirar Lamborghini Aventador Roadstar.

Tunde Ednut ne ya wallafa hotuna tare da bidiyon motar alfarmar a shafinsa a ranar Asabar da ta gabata.

Fitaccen sananne a shafukan sada zumuntar ya wallafa hoton tsohon dan majalisar yana tuka motarsa mai darajar dala miliyan daya wanda yayi daidai da N460,000,000.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel