Yadda aka halaka wani matashi kan budurwa a Kano

Yadda aka halaka wani matashi kan budurwa a Kano

- An kashe wani matashi, Sagir Muhammad a yankin Unguwar Sheka da ke karamar hukumar Kumbotso na jihar Kano

- An tattaro cewa wani matashi mai Abdullahi Muhammad ne ya halaka saurayin ta hanyar yi masa duka

- Hakan ya biyo bayan rigima da suka yi a kan wata budurwa da ke unguwar

Rahotanni sun kawo cewa wani abun tashin hankali ya afku a Unguwar Sheka da ke karamar hukumar Kumbotso na jihar Kano.

Mutanen wannan yanki dai sun tashi da alhini na mutuwar wani dan unguwar mai suna Sagir Muhammad wanda ake zargin wani matashi mai suna Abdullahi Muhammad da kashe shi.

Ana dai zargin Abdullahi da kashe Sagir Muhammad dan kimanin shekara 22 ta hanyar dukansa, sakamakon sabani da ya shiga tsakaninsu a kan wata budurwa, jaridar Aminiya ta Daily Trust ta ruwaito.

Yadda aka halaka wani matashi kan budurwa a Kano
Yadda aka halaka wani matashi kan budurwa a Kano Hoto: @dailytust
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Girman kai rawanin tsiya: An hango gwamnan Kwara yana yankar ciyawa

An tattaro cewa wani idon shaida da ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa rigima ce ta auku a tsakanin matasan biyu a kan wata budurwa da ke unguwar.

Majiyar ta ce bayan da lamarin ya faru an dangana da marigayin zuwa wata karamar cibiyar lafiya da ke unguwar ta Sheka inda kuma a nan ne rai ya yi halinsa.

Kakakin rundunar yan sandan ihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce yanzu haka suna gudanar da bincike a kai.

KU KARANTA KUMA: Daga ƙarshe: Ambasada Wali ya amince ayi sulhu tsakaninsa da Kwankwaso

A wani labari na daban, wata mata mai suna Hauwa da ke zama a kwatas ta Diso da ke karamar hukumar Gwale ta jihar Kano ana zarginta da yi wa 'ya'yanta biyu yankan rago.

Hakan ta faru bayan rikicin da ya auku tsakaninta da mijinta mai suna Ibrahim Haruna Aminu wanda bai dade da yin sabuwar amarya ba.

Jaridar Solacebase ta wallafa cewa, yaran da mahaifiyarsu ta yi wa yankan ragon su ne Yusuf Ibrahim mai shekaru 5 da kanwarsa Zahra'u mai shekaru uku.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel