Girman kai rawanin tsiya: An hango gwamnan Kwara yana yankar ciyawa

Girman kai rawanin tsiya: An hango gwamnan Kwara yana yankar ciyawa

- Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya nuna cewa shi jagora ne na gari taa hanyar aikatau

- AbdulRazaq ya wallafa hotunansa a yayinda yake yanka ciyawa a kwalejin Mount Carmel da ke Ilorin

- A cewar gwamnan, yana so ya karfafa wa mutane gwiwar kula da gine-ginen da yake mallakar gwamnati

Gabannin komawa makaranta a ranar Litinin, 5 ga watan Oktoba, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara, a ranar Asabar, 3 ga watan Oktoba, ya shiga sahun al’umman Oloje wajen yanke ciyawa a makarantar sakandare na Mount Camel.

Gwamna AbdulRazaq wanda ya wallafa hotunan a shafinsa na Twitter ya bayyana cewa idan gwamnati ta ajiye wani aiki a wani gari, hakkin mutanen garin ne su kula da shi tamkar nasu.

KU KARANTA KUMA: Bar murna karenka ya kama kura: Ƙusan APC ya ƙalubalanci nasarar Obaseki

Girman kai rawanin tsiya: An hango gwamnan Kwara yana yankar ciyawa
Girman kai rawanin tsiya: An hango gwamnan Kwara yana yankar ciyawa Hoto: @RealAARahman
Asali: Twitter

Ya ce ya aikata hakan ne domin karfafa wa mutane gwiwar kula da gine-ginen gwamnati da ke a yankunansu. Gwamnan ya bayyana cewa:

“Kasancewana a Oloje a yau shine domin nuni ga cewa babu wanda ya fi karfin shiga aikin gayya; ya kamata mu taimaki kanmu.”

KU KARANTA KUMA: Zaben shugaban ƙasa 2023: Magoya bayan Buhari na son Jonathan ya dawo mulki

A cewarsa, gwamnati na fama da karancin kudi saboda haka ba za ta iya jurewa ba.

Saboda haka ya yi kira ga al’umma da su hada hannu su bayar da taimakon da za su iya, domin ganin an tsaftace muhalli don gudun afkuwar annobar muhalli.

A wani labari na daban, Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a ranar Alhamis ya sanar da sakin fursunoni 25, rage wa'adin wasu ciki har da waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa da aka sauya musu zuwa ɗaurin rai da rai.

Gwamnan ya sanar da hakan ne cikin jawabinsa na bikin ranar cikar Najeriya shekaru 60 da samun ƴanci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng