Mutanen kasa sun yi martani bayan Buhari ya yi jawabin 1 ga Oktoba

Mutanen kasa sun yi martani bayan Buhari ya yi jawabin 1 ga Oktoba

- A jiya Najeriya ta cika shekaru 60 da samun ‘yancin-kai a hannun Birtaniya

- Shugaban kasa ya yi jawabi ga ‘Yan Najeriya kamar yadda aka saba a al’ada

- Wannan jawabi bai samu karbuwa ba musamman wajen masu bibiyar Twitter

Wannan karo ranar 1 ga watan Oktoba ta fado ne a ranar Alhamis, shugaba Muhammadu Buhari, ya yi wa jama’a jawabin murnar samun ‘yancin-kai a jiya.

Jim kadan da jawabin na shugaban Najeriyar, mutane su ka fito su na bayyana ra’ayoyinsu game da abin da Muhammadu Buhari ya fadawa ‘yan kasar ta sa.

Jaridar Vanguard ta ce mafi yawan martanin da aka samu ba masu dadi ba ne, da-dama su na ganin cewa jawabin jiya ya na cikin mafi muni na shugaban kasar.

Ga wasu kadan daga cikin abubuwan da mutanen kasar ke cewa a dandalin sada zumunta na Twitter:

KU KARANTA:

Mutanen kasa sun yi martani bayan Buhari ya yi jawabin 1 ga Oktoba
Shugaba Buhari ya na jawabin 1 ga Oktoba Hoto: Channels TV
Source: UGC

Kamala Obama ya rubuta: “Ina tunanin wannan ne mafi munin jawabin ranar ‘yancin kai da wani shugaban Najeriya ya taba yi a tarihi.”

Ose Anenih ya soki jawabin shugaban kasar, ya ce babu wani gyara da gwamnatinsa ta kawo a harkar zabe, sai dai ma yi wa bangaren shari’a katsalandan a harkokinta.

A cewar Malam Faruk Gangaran, abin da jawabin ya ke nufi shi ne, ko da litar man fetur za ta kai N300, za a samu uzurin da za a ba ‘Yan Najeriya. Ya ce: “Akwai sauran tafiya.”

Wata mai suna Tosin cewa ta yi, ba a taba yin shugaba kasar da ba ayi dacensa ba irin Muhammadu Buhari. Sai dai dinbin mutane ba za su yarda da wannan ba.

Karo Orovni, bai gamsu da jawabin shugaban kasar ba.

Kun ji cewa Muhammadu Buhari ya yi kokarin kare matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na kara kudin man fetur, ya ce ko a Saudi litar man fetur ta kai N168.

Bulama Bukarti ya ce idan za a rika biyan N305, 000 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikata a Najeriya, ‘yan kasar a shirye su ke su saye litar man fetur a N168.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel