Gwamnatin Kano ta sanar da ranar bude makarantun jihar

Gwamnatin Kano ta sanar da ranar bude makarantun jihar

- Kwamishinonin ilimi na jihohin arewacin Najeriya 19 sun amince cewa za a bude makarantun sakandire da firamare kafin ranar 31 ga watan Oktoba

- Jihohin Bauchi, Neja, da Yobe sun sanar da ranakun bude makarantun sakandire da firamare

- Sai dai, har yanzu babu sanarwa daga ma'aikatar ilimi ta tarayya da jihohi dangane da ranar bude makarantun gaba da sakandire

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa za a bude makarantu ma su zaman kansu da na gwamnati a ranar 11 ga watan Oktoba domin fara zangon karatu na uku a kakar 2019/2020.

Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Muhammad Sanusi Kiru, ne ya sanar da hakan yayin taro da manema labarai ranar Alhamis a ofishinsa.

Kiru ya shaidawa manema labarai cewa gwamnati ta yanke shawarar bude makarantu bayan kammala taro da ma su ruwa da tsaki da kuma biyo bayan taron kwamishinonin ilimi na jihohin arewa 19 da aka yi a Abuja.

A cewar kwamishinan, ana umartar dukkan malaman makaranta su koma bakin aikinsu a ranar 11 ga watan Oktoba.

A jiya, Laraba, ne Legit.ng Hausa ta wallafa labarin cewa gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bada umurnin bude dukkan makarantun firamare da sakandare ranar 12 ga Oktoba, 2020.

Kwamishanan ilimin jihar, Dr Muhammad Sani Idris a hirar da yayi da jaridar Leadership a Damaturu, ya ce gwamnatin jihar ta yi alhinin kulle makarantun sakamakon bullar cutar Korona.

A cewarsa gwamna Mai Mala Buni ya baiwa ma’aikatar ilimin jihar ta bude dukkan makarantun firamare da sakandare dake jihar ranar 12 ga Oktoba.

Yace: “Ina farin cikin sanar da cewa ranar Litinin, 12 ga Oktoba 2020, za a koma karatu a makarantun firamare da sakandare bayan bata tsawon lokaci.“

Ya tabbatar da cewa ma’aikatar ilimin ta shirya dukkan hanyoyin dakile yaduwar cutar bisa sharrudan da gwamnatin tarayya ta gindaya.

Ya shawarci iyaye su mayar da hankulansu kan kiwon lafiyan yaransu ta hanyar taimakawa makarantun wajen samar da kayayyakin yakar annobar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng