Yadda jaruman Kannywood suka yi murnar cikar Najeriya shekara 60 (hotuna)

Yadda jaruman Kannywood suka yi murnar cikar Najeriya shekara 60 (hotuna)

- Kasar Najeriya ta cika shekaru 60 da samun yancin kai a yau Alhamis, 1 ga watan Oktoba, 2020

- Manyan jaruman Kannywood basu bari an barsu a baya ba wajen raya wannan rana

- Jaruman masa'antar da dama sun wallafa sakon taya murna a shafukansu dauke da hotuna sanye da kaya kalar tutar Najeriya na kore da fari

A yau Alhamis, 1 ga watan Oktoba, 2020 ne yan Najeriya ke murnar cikar kasar shekaru 60 da samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka.

Dubban yan Najeriya na cike da murnar wannan rana duk da cewa akwai kalubale daban-daban da kasar ke fuskanta.

Saboda haka ne yan masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ma suka fito suna nuna nasu farin cikin.

Jaruman masa’antar da dama sun wallafa hotunansu da rubuce-rubuce domin raya wannan rana a shafukan soshiyal midiya.

Yadda jaruman Kannywood suka yi murnar cikar Najeriya shekara 60 (hotuna)
Yadda jaruman Kannywood suka yi murnar cikar Najeriya shekara 60 Hoto: real_maryamyahaya/realalinuhu/mansurah_isah
Source: Instagram

An gano jaruman sanye da tufafi launin tutar Najeriya, wato kore da fari.

Ga wasu hotuna da wasu fitattun jaruman na Kannywood suka wallafa a shafukansu na sada zumunta.

KU KARANTA KUMA: Mu farka: Yan bindiga sun kusa kutsawa Abuja - Dan majalisar tarayya ya koka

Fitaccen jarumi Ali Nuhu wanda aka fi kira da Sarkin Kannywood, ya wallafa wannan hoton tare da cewa: ''Yancin kai da yanci na gaskiya kan samu ne kawai ta hanyar yin abin da ya dace. A matsayinmu na yan Najeriya, kasarmu da muke kauna, muna bukatar yin abin da ya dace don ganin sauyin da ko yaushe muke magana a kansa ya samu. Kasarmu ta cika shekara 60, dole mu yi fafutuka a tare don tabbatar da martabarta.''

A nata sakon taya murnar samun yancin kai, Fati Washa ta wallafa: ''Ku zo mu daga hannu don murnar wannan ranar tare da yin bikinta. Ku zo mu tashi tsaye don nuna girmamawarmu ga jagororin da suka mutu a fafutukar nemo mana yanci. Ku zo mu rera takenkasarmu dauke da tutoci a hannayenmu don bikin wannan rana mai muhimmanci.''

KU KARANTA KUMA: Hankali ba zai dauka ba ace Saudi ta fi Najeriya arahar man fetur - Buhari

A bangarensa Sani Danja ya ce: ''Yaranmu na yau, shugabannin gagarumar kasarmu Najeriya. Barka da zagayowar ranar samun yancin kai Najeriya.''

Mansura Isah kuma ta wallafa: ”Babu wani waje da ya kai gida. Barka da zagayowar ranar samun yancin kan Najeriya.''

A nashi bangaren, Sadiq Sani Sadiq ya ce: ''Nigeria kasarmu ta gado. A cikinki aka haife mu a cikinki muka girma, ba mu da wata kasa da ta fi ki, a kullum muna alfahari da ke. Mun sani Allah ya albarkace ki da dumbin dukiya mai tarin yawa domin mu amfana, amma Kash! Allah ya jarrabe mu da shugabanni mafi yawan su azzalumai marasa kishin kasarsu, mu kuwa talakawan akasarin mu ba mu da godiyar Allah. Ke dai ga ki nan shekararki 60, amma kina nan ba ki canza ba, muna rokon Allah ya ba mu ikon sauya halayenmu da mu da shugabannin kasarmu baki ɗaya. Barka da zagayowar ranar samun yancin kan Najeriya."

Saratu Gidado ta wallafa: ''Ina yi wa dukkan yan Najeriya murnar zagayowar ranar samun yancin kan kasarmu.

A sakon Maryam Yahaya ta ce: “Barka da zagayowar ranar samun yancin kai Najeriya.''

A gefe guda, a ranar Alhamis, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa kasar nan tana cikin mawuyacin hali a fannin tattalin arziki.

Ya ce hakan kuwa daidai yake da kowacce kasa domin kuwa dukkan duniya ne ake cikin wannan halin.

Buhari ya sanar da hakan ne a jawabinsa ga 'yan Najeriya a ranar da kasar ta cika shekaru 60 da samun 'yancin kai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel