Najeriya @60: DSS sun tarwatsa ma su zanga-zanga, sun kama wasu a Osun

Najeriya @60: DSS sun tarwatsa ma su zanga-zanga, sun kama wasu a Osun

- Wasu matasa sun shirya fara gudanar da zanga-zangar juyin juya hali a ranar da Najeriya ta cika shekaru 60 da samun 'yanci

- Ma su zanga-zangar na neman a mayar da ilimi kyauta tare da kawo karshen cin hanci a Najeriya

- Sai dai, jami'an tsaro sun yi amfani da karfi domin tarwatsa ma su zanga-zangar tare da kama wasu daga cikinsu

Wata tawagar jami'an tsaro na farin kaya (DSS) sun tarwatsa gungun wasu matasa da su ka fito domin gudanar da zanga-zangar juyin juya hali saboda wahalar da 'yan Najeriya ke sha.

Tun da sanyin safiyar ranar Alhamis jami'an tsaro su ka mamaye filin taro na Nelson Mandela Freedom Park da ke Osogbo domin hana ma su zanga-zangar yin amfani da wurin a matsayin matattararsu, kamar yadda su ka tsara.

Amma duk da kasancewar jami'an tsaro dauke da makamai, hakan bai hana ma su zanga-zangar su hadu a wurin tare da fara gudanar da tattaki ba.

DUBA WANNAN: Wata sabuwa: Ana shirin murnar Nigeria @60, gwamnatin Ogun ta sanya dokar ta baci

Sai dai, jami'an tsaro sun yi amfani da karfi domin tarwatsa ma su zanga-zangar a yayin da su ka isa shataletalen Old Garage.

Najeriya @60: DSS sun tarwatsa ma su zanga-zanga, sun kama wasu a Osun
Ma su zanga-zanga a Osun
Source: UGC

Najeriya @60: DSS sun tarwatsa ma su zanga-zanga, sun kama wasu a Osun
Zanga-zanga a Osun
Source: UGC

Kafin a tarwatsasu tare da kama kusan goma daga cikinsu, ma su zanga-zangar sun gudanar da wakokin neman a mayar da ilimi kyauta tare da kawo karshen cin hanci a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa daruruwan masu zanga-zanga a ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoba, sun mamaye wasu unguwannin jihar Lagas domin nuna rashin jin dadinsu a kan tabarbarewar shugabanci a Najeriya.

DUBA WANNAN: Babbar magana: Buhari ya yi amai ya lashe ana gobe bikin Nigeria @60

Masu zanga-zangan sun yi tattaki daga unguwannin Ojota zuwa Maryland a Lagas. An gano su suna wake-wake.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa jami’an tsaro sun kama masu zanga-zangar akalla su 30.

Gamayyar masu zanga-zangar na juyin-juya hali a cikin wata sanarwa da suka saki kafin zanga-zangar, sun yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi murabus.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel