Jawabin Buhari: A gani a kasa ya fi fadi da fatar baki, In ji Jega

Jawabin Buhari: A gani a kasa ya fi fadi da fatar baki, In ji Jega

- Tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega ya yi martani ga jawabin Shugaban kasa Buhari na ranar yancin kai karo na 60

- Jega ya ce tabbass shugaban kasar ya tabo muhimman batutuwan da ya kamata, amma cewa kamata yayi a aiwatar da su ba wai a fade su ba kawai

- Farfesan ya kuma tabbatar da cewar Najeriya ta yi nisa a cikin shekaru 60 da suka gabata

Tsohon Shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega na so a ga abubuwan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadi a jawabinsa na ranar yancin kai a kasa, ba wai ya tsaya a fatar baki ba kawai.

Tsohon Shugaban na INEC ya yi magana ne a ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoba, a lokacin wani shiri na musamman na gidan talbijin din Channels domin bikin cikar Najeriya shekaru 60.

“Abunda yake a bayyane shine cewa jawabin nasa na dauke da abubuwa da dama da suka dace a fade su a irin wannan rana.

“Ina ganin yana da matukar muhimmanci ayi magana kan abunda ya kamata gwamnati tayi domin tabbatar da ganin cewa a duk lokacin da aka yi kira ga yan Najeriya don yin alfahari da Najeriya, sai ya zamana akwai wasu abubuwa da za su karfafa masu gwiwa da taimaka masu wajen aikata hakan.”

KU KARANTA KUMA: Dan majalisar PDP tilo na jihar Yobe sauya sheka zuwa APC

Yayinda ya yarda cewa Najeriya ta yi nisa a cikin shekaru 60 da suka shige, farfesan ya yi kira ga yin taka tsan-tsan, inda yace lallai bikin yancin kai na 60 ya zama lokaci na tunani.

“Shakka babu a cewa Najeriya ta yi nisa a shekaru 60 da suka gabata, amma kuma yana da matukar muhimmanci kada a kasance a yanayi na biki, maimakon haka kamata yayi ayi amfani da lokacin a matsayin na tunani cikin tsanaki a kan abunda muke so Najeriya ta zama a shekaru 60 masu zuwa,” Jega ya yi bayani.

Jawabin Buhari: A gani a kasa ya fi fadi da fatar baki, In ji Jega
Jawabin Buhari: A gani a kasa ya fi fadi da fatar baki, In ji Jega Hoto: @PremiumTimesng
Source: UGC

Jega ya ce koda dai kasar na fuskantar matsaloli da dama, ya kamata jawabin Buhari ya zaburar da wadanda ke kan mulki ta yadda za su yi abubuwan da zai karfafa wa al’umman kasar gwiwa.

KU KARANTA KUMA: Rashin nada sabon Sarki ya jefa Zariya cikin dar-dar da tashin hankali

A gefe guda, a yammacin ranar Laraba, Buhari ya sanar da cewa ba zai gabatar da jawabi ga yan Nigeria a dandalin Eagle Square kamar yadda ya yi niyya a baya ba.

Haka zalika, shugaban kasar ya sanar da cewa, a yanzu zai gabatar da jawabin ne kai tsaye ga 'yan kasar ta talabijin daga fadar shugaban kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel