Wata sabuwa: Ƴan ta'adda sun kashe sojojin Nigeriya 10 a harin kwantan ɓauna

Wata sabuwa: Ƴan ta'adda sun kashe sojojin Nigeriya 10 a harin kwantan ɓauna

- Mayakan ISWAP sun kashe dakarun sojojin Najeriya goma a garin Marte da ke yankin tafkin Chadi

- Majiyoyi sun bayyana cewa tawagar motocin sojin na a hanyarsu na kai wa dakarun da ke yankin kayayyakin amfani lokacin da mayakan suka kai masu harin bazata

- Har ila yau sojoji takwas sun jikkata a harin

Mayakan ta’addanci masu ikirarin jihadi sun halaka dakarun sojojin Najeriya 10 a wani harin bazata da suka kai kusa da garin Marte da ke yankin tafkin Chadi, wasu majojin tsaro biyu suka bayyana a ranar Laraba.

Mayakan ISWAP dauke da bindigogin toka da kananan bama-bamai a ranar Talata, sun budewa wata tawagar sojoji wuta a hanyarsu na rabon kayayyaki, jaridar The Guardian ta ruwaito.

“Yan ta’addan sun kashe sojoji 10, ciki harda manyan jami’ai biyu, a harin bazatan,” daya daga majiyoyin taa sanar da AFP.

KU KARANTA KUMA: Kwana daya bayan rasuwar tsohon Sarki: An nada sabon Sarkin Kuwait

Hakazalika majiyar ta bayyana cewa sojoji takwas sun jikkata a harin.

Wata sabuwa: Ƴan ta'adda sun kashe sojojin Nigeriya 10 a harin kwantan ɓauna
Wata sabuwa: Ƴan ta'adda sun kashe sojojin Nigeriya 10 a harin kwantan ɓauna Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Tawagar na a hanyarsu na zuwa kai wa dakarun sojin da ke yankin abinci da sauran kayayyaki lokacin da aka kai masu hari, in ji majiyar wacce ta nemi a boye sunanta.

An kuma tattaro cewa yan ta’addan sun sace kayayyakin sannan suka sanya wa manyan motoci biyu wuta kafin suka tsere cikin jeji.

Sun bayyana cewa harin na iya zama ramuwar gayya ga tayar da sansanin yan ta’addan da aka yi a yankin Marte, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mambobinsu da dama, ciki harda kwamandoji uku.

Mayakan ISWAP dai sun balle ne daga Boko Haram a 2016.

KU KARANTA KUMA: Babbar magana: Yadda shugabannin ƙanana hukumomi biyu suka ba hammata iska

A gefe guda, mun ji cewa kwamishinan shari’a na jihar Borno, Kaka Lawan, ya yi bayanin yadda mayakan Boko Haram suka kai wa gwamnan jihar, Babagana Zulum hari.

Lawan ya ce an fara kai wa gwamnan hari ne da abubuwan fashewa da aka dasa a hanyar da tawagarsa za su bi, sannan ya ce an kai hari na biyu ne ta hanyar daura wa jaki bam.

Yan ta’addan Boko haram sun kai wa Zulum wasu hare-hare mabanbanta har guda biyu cikin yan kwanakin da suka gabata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel