Momoh: Gwamnatin Tarayya ta dakatar da karin farashin shan wutar lantarki

Momoh: Gwamnatin Tarayya ta dakatar da karin farashin shan wutar lantarki

- NERC ta umarci DisCos su dakata da batun karin farashin shan wutar lantarki

- An dauki wannan mataki ne a sakamakon zaman ‘yan kwadago da Gwamnati

- Yarjejeniyar ita ce za a janye karin kudin wuta har zuwa nan da makonni biyu

Hukumar da ke kula da harkar wuta, NERC ta umarci kamfanonin da ke raba wuta wadanda aka fi sani da DisCos, su dakatar da karin kudin wuta.

Jaridar Daily Trust ta ce NERC ta bada umarni a janye karin farashin shan wutar lantarkin da aka yi a Najeriya a ranar Talata, 1 ga watan Satumba, 2020.

NERC ta bukaci kamfanonin da ke da alhakin raba wuta su janye wannan kari na tsawon makonni biyu.

KU KARANTA: Buhari ya yi nadin mukamai a gidan wuta

Hukumar ta fitar da wannan umarni ne a ranar Talata, 30 ga watan Satumba, 2020. Shugaban NERC, Farfesa James Momoh ya sa hannu a takardar jiyan.

James Momoh ya ce daga ranar 28 ga watan Satumban 2020 zuwa 11 ga watan Oktoban bana, DisCos za su saida wutar lantarki ne a kan tsohon farashi.

Momoh a wannan takarda, ya ce kamfanonin da ke kasar nan za su saida wuta ne kamar yadda su ka saba saidawa har zuwa ranar 31 ga watan Agusta, 2020.

Hakan na nufin nan da mako biyu masu zuwa, rukunin mutanen da aka yi wa karin sama da 100% na kudin wuta, za su samu damar shan wutan a farashin da.

KU KARANTA: Buhari ya tura sunan wanda za a ba mukami, An samu ‘Yan Majalisa sun ce a'a

Momoh: Gwamnatin Tarayya ta dakatar da karin farashin shan wutar lantarki
Shugaban NERC, Momoh Hoto: Twitter/NERCNG
Asali: Twitter

Momoh ya ce: “Duk wutan da za a saidawa mutane a tsawon kwanakin nan 14, ya zama a kan farashin yadda ake saida wutan a ranar 31 ga watan Agusta, 2020.”

Sashe na 33 na dokar wuta ta EPSRA 2005, ta ba Ministan harkokin wuta damar da zai iya bada umarni ga hukumar NERC ta sa a rage farashin wutar lantarki.

Hukumar ta dauki wannan mataki ne a sakamakon zaman da aka yi tsakanain shugabannin ‘yan kwadago da gwamnati, inda aka yarda a fasa shiga yajin-aiki.

Idan za ku tuna, sakataren gwamnati da Ministan wuta Sale Mamman sun halarci zaman.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel