Masu zargin gwamnatin Buhari da cin rashawa manyan 'yan adawa ne - Lawan

Masu zargin gwamnatin Buhari da cin rashawa manyan 'yan adawa ne - Lawan

- Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan yace masu caccakar gwamnatin Buhari akan rashin yaki da rashawa 'yan adawa ne

- A cewarsa, babu gwamnatin da ta jajirce wurin yaki da rashawa a kasar nan kamar wannan

- Yace akwai gwamnatin da har ta fara ta kare bata taba tsawatarwa ba akan rashawa

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ce masu zargin gwamnatin Buhari da rashawa 'yan adawa ne.

Yayi maganar ne a taro na biyu da aka yi akan yaki da rashawa wanda ICPC ta shirya, Lawan ya ce gwamnatin Buhari ta jajirce wurin yaki da rashawa.

Shugaban majalisar tarayya ya ce a tuna lokacin da gwamnatin baya ta kira rashawa da "sata kawai".

Yace, "Ban san su ba, kuma ban san me suka dogara dashi ba. Kuma ba zanyi amfani da jita-jita ba, zanyi amfani da gaskiyar lamari ne. Ina so a nuna min ta inda rashawar wannan gwamnatin yafi na waccan.

"Idan zaku tuna, a gwamnatin baya akwai wanda ya kira cin hanci da sata kadai.

"Wannan gwamnatin bata taba kama wani da laifin rashawa ba ta bar shi haka nan ba tare da an hukunta shi ba. Don haka sai dai idan mutum dan adawa ne, to zai iya fadin komai."

"Idan mutum dan adawa ne, zai iya cewa wannan gwamnatin tafi waccan kyale rashawa.

"Ba don ina tare da wannan gwamnatin ba, zan iya fadar cewa abubuwa 3 wannan gwamnatin tafi mayar da hankali, yaki da rashawa, yaki da ta'addanci sai skuma tabbatar da tsaro a kasar nan da kuma bunkasa tattalin arziki.

"A tarihi babu wata gwamnati da aka taba yi a Najeriya da ta taba yaki da rashawa irin wannan. Akwai gwamnatin da har ta fara kuma ta kare bata taba magana akan cin hanci ba.

"Wannan gwamnatin ta jajirce wurin yakar rashawa, kuma ina so a san cewa, duk wadanda suke cewa gwamnatin nan bata yaki da rashawa, to kawai dan adawa ne," yace.

KU KARANTA: Magidanci ya halaka kwarton matarsa bayan kama su da yayi suna lalata a kan gadonsu na aure

Masu zargin gwamnatin Buhari da cin rashawa basu da amfani - Lawan
Masu zargin gwamnatin Buhari da cin rashawa basu da amfani - Lawan. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Allah ke ciyarwa, zan cigaba da haihuwa - Mutumin da ke da 'ya'ya 19 (Bidiyo)

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace yana fatan babu wani dan Najeriya da zai wahala koda a wacce jam'iyya yake.

Shugaban kasar ya fadi hakan ne lokacin da Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya raka mataimakinsa, Philip Shuaibu da wasu yan jam'iyyarsu don godiya ga shugaban kasar a Abuja.

Shugaba Buhari ya sha alwashin kokarta wa wurin ciyar da al'umma gaba a bisa gaskiya da amana. Sannan ya roki jama'a dasu dage wurin bada hadin kai ga gwamnati don samun cigaban kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel