A ƙarshe: Gwamna Zulum ya magantu kan harin da Boko Haram ta kai masa har sau biyu

A ƙarshe: Gwamna Zulum ya magantu kan harin da Boko Haram ta kai masa har sau biyu

- A ƙarshe Gwamna Zulum ya yi martani kan harin da Boko Haram ta kai masa har sau biyu

- Zulum ya jaddada cewa zai kara yin taka-tsan-tsan kan yadda yake aiwatar lamuran gwamnatinsa don ganin ya dawo da zaman lafiya a jihar Borno

- Zulum ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin yan majalisar dokokin tarayya daga Borno

Biyo bayan hare-haren kwanan nan da aka kai wa tawagarsa, gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya ce zai “kara taka-tsan-tsan” game da yadda yake aiwatar da jajircewar gwamnatinsa na dawo da zaman lafiya a dukkanin garuruwan jihar.

Zulum ya bayar da wannan tabbacin ne ga mambobin majalisar dokokin tarayya daga Borno, wadanda suka kai masa ziyarar jaje kan hare-haren da aka kai masa kwanan nan.

Akalla jami’an tsaro 15 da suka hada da sojoji, yan sanda da yan sa-kai na JTF ne suka rasa rayukansu a harin na makon da ya gabata, yayinda wasu takwas suka jikkata.

Mambobin majalisar dokokin karkashin jagorancin tsohon gwamnan Borno kuma sanata mai ci a yanzu, Kashim Stettima, sun nuna alhininsu ga gwamnan.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Majalisar Dattijai ta dawo bakin aiki bayan hutun makonni takwas

A ƙarshe: Gwamna Zulum ya magantu kan harin da Boko Haram ta kai masa har sau biyu
A ƙarshe: Gwamna Zulum ya magantu kan harin da Boko Haram ta kai masa har sau biyu Hoto: @channelstv
Source: Twitter

Sun kuma yi addu’a ga dukkanin jami’an tsaron da suka rasa rayukansu a yayin arangama da yan ta’addan.

Gwamna Zulum wanda ya nuna farin ciki da ziyararsu, ya bayyana cewa hakan alamun hadin kai da goyon baya ne a gare shi, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Sai dai kuma ya bayyana cewa hakan ba zai sanyaya masa gwiwa ba a jajircewasa na dawo da zaman lafiya a jihar Borno nan da dan wani lokaci kadan.

Gwamnan ya ce har yanzu halin da jihar ke ciki na da matukar hatsari musamman ta fuskacin shi kansa da wadanda suka yi masa rakiya zuwa yankunan arewacin jihar Borno.

KU KARANTA KUMA: Ku sani: Dalilin da ya sa gwamnatin Kano ta kama jarumin Kannywood, Naburaska

Zulum ya kara da cewa gwamnatinsa na burin dawo da zaman lafiya a gabar tekun Chadi, yankin Sambisa da tsaunukan Mandara, wanda ke samar da albarkatun gona ga manoman karkara a jihar.

A gefe guda, Zulum ya ziyarci iyalan 'yan sanda da 'yan kungiyar sintiri na JTF da yan ta'adda suka kai wa hari a ranar Juma'a a hanyarsu ta zuwa Baga.

Zulum ya ziyarci hedkwatan 'yan sanda na jihar Borno da ke Maiduguri inda iyalan wadanda suka rasu suka taru domin tarbansa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel