Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da tallafin CCT a Jihar Bayelsa
- Shirin CCT na rabawa marasa karfi kudi ya shiga wasu garuruwan Jihar Bayelsa
- Minista Sadiya Umar-Faruk ta kaddamar da shirin a Ekeremor, Nembe da Ijaw
- Wannan ya na cikin kokarin gwamnatin tarayya na rage radadin talauci a Najeriya
Ministar bada tallafi da agaji da cigaban al’umma, Hajiya Sadiya Umar-Faruk, ta kaddamar da shirin CCT na gwamnatin tarayya a jihar Bayelsa.
Sadiya Umar-Faruk ta ce gwamnati za ta rika biyan marasa hali N5000 duk wata a Bayelsa.
Gwamnatin tarayya ta kan zabi Bayin Allah da su ka fi kowa jikkata domin ta taimaka masu da abin da za su rike rayuwarsu a tsarin nan na CCT.
KU KARNTA: Cire mutum miliyan 100 daga talauci zai yi wahala - Sani
Daily Trust ta ce an kaddamar da wannan shiri yanzu a cikin kananan hukumomi uku a jihar; Ekeremor, Nembe da karamar hukumar Ijaw ta Kudu.
Jaridar ta fitar da rahoto a ranar 28 ga watan Satumba, 2020 cewa Temitope Sinkaiye ce ta wakilci mai girma minista, wajen kaddamar da shirin a jiya.
Makasudin shirin shi ne a rage radadin talauci musamman a cikin mata da marasa galihu a jihar kamar yadda Minista, Sadiya Umar-Faruk ta bayyana.
Temitope Sinkaiye a madadin Ministar ta kara da cewa wannan tsari na CCT ya na cikin shirye-shiryen NASSCO da aka kawo domin masu karamin karfi.
KU KARANTA: Buhari zai raba motoci a sakamakon karin farashin man fetur
“Dabbaka tsare-tsaren gwamnatin tarayya na fitar da jama’a daga talauci ya taikmakawa ‘yan Najeriya, musamman talaka da kuma marasa galihu.”
A sakamakon haka, ministar bada tallafi da agajin ta ce talakawa sun ga tasirin gwamnatin APC mai-ci da shugaba Muhammadu Buhari ya ke jagoranta.
Kamar dai yadda ku ka sani, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kudiri niyyar fito da mutane miliyan 100 daga cikin talauci a fadin Najeriya.
Kwamishinar harkokin mata, Faith Opuene ta wakilci gwamnan Bayelsa, Douye Diri a taron.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng