Saudiyya: Mun gano wata babbar maɓuyar ƴan ta'adda

Saudiyya: Mun gano wata babbar maɓuyar ƴan ta'adda

- Hukumar kasar Saudiyya ta sanar da tarwatsa wata mabuyar yan ta’ adda da ta gano

- Gwamnatin kasar ta kama mutum goma tare da kwace makamai da abubuwan fashewa

- Sai dai babu wani cikakken bayani a kan yankin da aka gano mabuyar yan ta’addan

Gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da yin watsa-watsa da wata mabuyar wasu ta’ adda da ta gano a cikin wannan wata.

Ta bayyana cewa ta kama mutane 10 tare da karbe makamai da abubuwan fashewa, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: An cafke mata da miji da mutane biyu dauke da kokon kan mutum a Ogun

An tattaro cewa kafafen watsa labarai na kasar sun ambato wata sanarwa daga gwamnatin na cewa mutum uku da aka kama sun samu hoto ne daga dagakarun juyin juya halin Iran, sauran kuma suna da alaka da gidan gona da aka gano.

Saudiyya: Mun gano wata babbar maɓuyar ƴan ta'adda
Saudiyya: Mun gano wata babbar maɓuyar ƴan ta'adda Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sai dai kuma babu wani cikakken bayani game da yankin da aka gano mabuyar yan ta'addan.

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun sace darekta a gwamnatin jihar Zamfara tare da wasu mutane 5

A wani labari na daban, dakarun sojojin saman Najeriya sun lalata mabuyar 'yan ta'addan Boko Haram sannan sun kashe da dama cikinsu a Bula Sabo da Dole a jihar Borno.

Sun samu nasarar yin hakan ne sakamakon hare-haren da suka kai da jiragen yakin sama a ranar 23 ga watan Satumba don kaddamar da sabon atisaye mai suna 'Hail Storm 2' da aka kaddamar don tarwatsa 'yan Boko Haram da ke Tafkin Chadi da Dajin Sambisa.

Wannan na cikin sanarwar da kakakin hedkwatar tsaro na kasa, Manjo Janar John Enenche ya fitar a shafin hukumar na Twitter a ranar Juma'a 25 ga watan Satumba.

Ya ce an kai hare-haren ne bayan samun sahihan bayannan sirri da ke tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun samu mafaka a wasu gine-gine da ke dajin inda wasu kwamandojinsu ke buya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel