Katsina da Zamfara: 'Yan bindiga 32 sun shiga hannu, an kashe 1 - DHQ

Katsina da Zamfara: 'Yan bindiga 32 sun shiga hannu, an kashe 1 - DHQ

- Rundunar dakarun OSS ta tabbatar da damke 'yan bindiga 32 tare da kashe wani daya daga ciki

- Kamar yadda shugaban rundunar ya sanar, ya ce sun yi wannan nasarar ne tsakanin 18 zuwa 24 ga watan Satumba

- Rundunar ta tabbatar da ceto wata mata mai suna Jamila Sani daga hannun 'yan bindigar tare da tarwatsa sansaninsu

Rundunar dakarun OSS, sun kashe dan bindiga 1, sun kama 11 da kuma masu hada kai dasu guda 20, cikinsu harda masu kai musu miyagun kwayoyi. Hakan ta faru tsakanin 18 zuwa 24 ga watan Satumba 2020.

Rundunar sun ceci wata mata mai suna Jamila Sani, sun kuma tarwatsa sansanin su dake jihohin guda biyu a cikin kankanin lokaci.

Shugaban rundunar, Birgediya Janar Bernard Onyeuko, ya sanar da hakan a ranar Lahadi a Katsina.

Ya ce a cikin abubuwan da aka kama yan ta'addan dasu akwai bindigogi, adduna da wukake.

Onyeuko, wanda ya sanar da wannan cigaban, ya ce, "Ranar 18 ga watan Satumba 2020, rundunar jami'an tsaron da aka wakilta a Dangulbi, sun kama wasu Umaru Lawali da Ahmed Bello, a lokacin da suka je sintiri."

"Sannan rundunar da aka tura kwatarkwashi a jihar Zamfara, sun kama wani Yunusa Muhammad a Gidan Yawa da ke karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara.

Wadanda ake zargi sun tabbatar da cewa su kwararru ne a harkar garkuwa da mutane da amsar kudade," a yadda aka wallafa

KU KARANTA: Jerin kasashe biyar a duniya da suke da saukin samun aiki

Katsina da Zamfara: 'Yan bindiga 32 sun shiga hannu, an kashe 1 - DHQ
Katsina da Zamfara: 'Yan bindiga 32 sun shiga hannu, an kashe 1 - DHQ. Hoto daga Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda aka kama dan shekara 16 da bindiga a makarantar sakandare

A wani labari na daban, samamen da dakarun sojin sama na rundunar Operation Lafiya Dole karkashin Operation Hail Storm 2 suka aiwatar suke aiwatar ya cigaba da bada sakamako mai kyau.

Na karshen da ya faru shine ragargaza sansanin mayakan ta'addanci da kuma halaka wasu daga cikin 'yan Boko Haram da ke Tongule, Bone da Isari B Musa a ranar 24 ga watan Satumban 2020.

Samamen da dakarun suka kai Tongule an kai shi ne sakamakon tabbacin da suka samu na cewa 'yan ta'addan na zama a yankin da dare kadai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng