Kano ta yi babban rashi: Tsohon babban Alkalin jihar, Shehu Atiku, ya rasu

Kano ta yi babban rashi: Tsohon babban Alkalin jihar, Shehu Atiku, ya rasu

- Tsohon babban alkalin jihar Kano, Justis Shehu Atiku, ya rasu

- Marigayin ya amsa kiran mahaliccinsa a ranar Lahadi, 27 ga watan Satumba, bayan ya yi yar gajeruwar jinya

- Wata majiya a gwamnatin jihar Kano ta ce labarin mutuwar ya daki Gwamna Abdullahi Ganduje sosai

Allah ya yiwa tsohon babban alkalin jihar Kano, Justis Shehu Atiku rasuwa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shehu Atiku ya rasu ne a ranar Lahadi, 27 ga watan Satumba, bayan ya yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya.

Kakakin bangaren shari’a na jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa za a binne babban alkalin a yau Litinin, da karfe 10:00 na safe.

KU KARANTA KUMA: Kwanaki 8 babu sabon sarki: Ana zaman jiran tsammani a garin Zazzau

Kano ta yi babban rashi: Tsohon babban Alkalin jihar, Shehu Atiku, ya rasu
Kano ta yi babban rashi: Tsohon babban Alkalin jihar, Shehu Atiku, ya rasu hOTO: @dailytrust
Source: Twitter

Marigayi Justis Shehu Atiku ya yi ritaya daga aiki a watan Janairun 2015.

Majiyoyi sun ce za a rika tunawa da marigayin saboda irin rawar ganin da ya taka a shari’ar wasu bankuna da suka durkushe duk da kokarin bashi toshiyar baki da suka yi.

Wata majiya a gwamnatin jihar Kano ta ce Gwamna Abdullahi Ganduje ya shiga dimuwa kan rasuwar alkalin.

KU KARANTA KUMA: Ba ruwan Boko Haram: Waɗanda suka kaiwa tawagar Zulum hari sun fito sun magantu

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmed El Rufai, ya bayyana cewa tun ranar da marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Abubakar Shehu Idris, ya rasu, ba ya iya bacci sai ya sha magani saboda tsananin baƙin ciki.

Gwamnan ya bayyana hakan ne wajen taron addu'ar sadakar uku na Marigayin da ya gudana yau Laraba, 23 ga Satumba, 2020, BBC ta ruwaito.

Manyan mutane da dama sun halarci taron addu'ar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel