ACF ta ce Sojoji da Gwamnati su na da tambayar amsawa a kan harin Zulum
- Kungiyar Dattawan Arewa ta yi magana bayan an kai wa Gwamnan Jihar Borno hari
- Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce dole a kare ran Gwamna Babagana U. Zulum
- Emmanuel Yawe ya koka da yadda sojojin Boko Haram ke cigaba da ta’adi har yanzu
Kungiyar dattawan Arewa ta bayyana cewa gwamnatin tarayya da jami’an sojoji su na da tambayoyin da za su amsa kan harin da aka kai wa gwamnan Borno.
ACF ta yi magana ne a sakamakon harin da aka sake kai wa Farfesa Babagana Umara Zulum.
Mai magana da yawun bakin kungiyar ACF, Emmanuel Yawe, ya fitar da jawabi bayan ‘yan ta’adda sun kuma aukawa tawagar gwamnan a karshen makon da ya gabata.
A jiya jaridar Daily Trust ta rahoto Emmanuel Yawe ya na cewa harin ya sa shakku a kallon da ake yi wa sojojin Najeriya na cewa su na da karfin da za su kare kasar nan.
KU KARANTA: Zulum zai dauki mataki bayan an kai masa hari
Wannan kungiya ta manyan Arewa ta nuna dar-dar dinta na yadda 'Yan Boko Haram su ke cigaba da kai hare-hare duk da kwarin gwiwar da sojoji su ke kokarin badawa.
AFC ta ce harin da aka kai wa gwamnan Borno ya na zuwa ne jim kadan bayan an hallaka wani babban jami’in sojan kasa, Kanal CD Bako, a Damboa, duk a jihar ta Borno.
Yawe ya ce: “Mu na kira ga sojoji su yi maza, su yi kokarin dawo da yardar da aka yi masu. ACF ta na sane da yadda gwiwar jami’an tsaro da ke yaki ya ke sacewa.”
“Dole gwamnatin tarayya da jami’an tsaro su yi maza-maza, su yi maganin duk abubuwan da su ka jawo rashin kwarin gwiwar nan.” Inji mai magana a madadin ACF.
KUU KARANTA: Zulum ya ce akwai hannun sojoji a ta'adin da ake yi
Har ila yau, kungiyar ta ce dole a kare gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum.
A cewar Yewa, idan har ‘yan ta’adda su ka kai ga taba Mai girma gwamna Babagana Umara Zulum, babu shakka abubuwan da za su biyo baya ba za su yi kyau ba.
Idan za ku tuna an kai wa tawagar Gwamna Zulum hari a garin Baga, kuma mun ji cewa adadin Jami’an tsaron da su ka rasu wajen kare Gwamnan sun kai mutum 20
Ba wannan ne karon farko da sojojin Boko Haram su ka kai wa Babagana Umara Zulum hari ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng