Osinbajo ya bayyana lokacin bude iyakokin kasar nan

Osinbajo ya bayyana lokacin bude iyakokin kasar nan

- Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasar Najeriya ya ce nan babu dadewa za a bude iyakokin kasar nan

- Tun a watan Oktoban shekarar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin rufe iyakokin kasar nan

- Ya ce ba za a bude iyakokin ba har sai kwamitin da suka nemi a rufe sun sake zaunawa tare da tabbatar da cewa za a iya budewa

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce akwai sa ran gwamnatin tarayya ta bude iyakokin kasa nan kusa.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bada umarnin rufe iyakokin kasa a watan Oktoba 2019 saboda hana shigowa da kaya da makamai Najeriya, da kuma kiyaye kasuwancin cikin kasa.

Shuwagabannin kasashe kamar Ghana da jamhuriyar Benin sunyi ta rokon shugaban kasa akan ya taimaka ya bude iyakar, amma ya runtse idanunsa yace sam ba zai bude ba har sai kwamitin da ta zartar da rufewar ta duba lamarin.

Ya ce har sai kasashen da ke makwabtaka da Najeriya sun dakatar da barin kayan sumogal suna shigowa daga iyakarsu.

Osinbajo ya fadi hakan ne ranar Alhamis a lokacin da yake amsa tambaya akan bude iyakokin kasa.

Inda ya amsa da cewa, gwamnatin tarayya na nan tana tattaunawa da kasashen dake makwabtaka da Najeriya akan bude iyakoki.

Osibanjo yayi maganar ne a wani taro da The Africa Report suka shirya, saboda tattaunawa akan yadda za'a ciyar da Najeriya gaba, daga yadda Covid-19 ta dakatar da al'amuran kasa.

KU KARANTA: Sultan Hassanal Bolkiah: Hamshakin mai arzikin da ya mallaki Rolls Royce 500, N7m kudin askinsa

Osinbajo ya bayyana lokacin bude iyakokin kasar nan
Osinbajo ya bayyana lokacin bude iyakokin kasar nan. Hoto daga @Thepunch
Source: Twitter

Ya ce, "mu da makwabtanmu muna kokari a kan bude iyakokin kasa, yanzu haka muna sintiri tsakanin iyakokin, kuma muna ganin amfanin hakan. Ban tabbatar da lokacin da za'a bude ba amma nan kusa, zamu bude iyakokin.

"Mun mayar da hankali a kan AFCFTA amma munfi damuwa da rashin tsaron da kuma barakar arziki, shiyasa muka dauki matakan da zasu kare kasa.

"Ba har abada bane zamu cigaba da rufe iyakokin kasa ba, muna kokarin ganin yiwuwar bude su nan kusa."

KU KARANTA: El-Rufai ya yi watsi da 'yan takarar da majalisar nadin sarkin Zazzau suka bada, ya bada dalili

A wani labari na daban, wasu mayakan ta'addancin Boko Haram tare da iyalansu sun mika wuya ga dakarun sojin Najeriya a Banki.

Kamar yadda hedkwatar tsaro ta wallafa, ta bayyana hotunan mayakan ta'addancin tare da iyalansu da suka mika wuya ga dakarun sojin Najeriya.

Mayakan ta'addancin tare da iyalansu sun mika kansu ne ga bataliya ta 155 da ke Banki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel