"Ayo Salami ya na kukan dama bai karbi aikin binciken Ibrahim Magu ba"
- Ayo Salami ya na takaicin zama shugaban kwamitin da ke binciken EFCC
- Tsohon Alkalin ya koka da yadda ya jefa kansa a rikici bayan ya yi ritaya
- Wasu Lauyoyin da su ka zauna da Ayo Salami ne su ka bada wannan labari
Ayo Salami ya ce ya yi nadamar karbar shugabancin kwamitin shugaban kasa na binciken tsohon shugaban hukumar EFCC, Mista Ibrahim Magu.
Wasu lauyoyi biyu su na wurin da tsohon Alkalin ya bayyana haka kamar yadda jaridar Premium Times ta bayyana a ranar Lahadi, 27 ga Satumba, 2020.
Tsohon Alkalin babban kotun daukaka karar kasar ya yi wannan kuka ne a ranar Juma’a a lokacin da ya ke sauraron masu kare Ibrahim Magu.
Wannan kwamiti na Ayo Salami ya na zama ne fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja.
KU KARANTA: Hadimin Buhari, Sagay ya yi Allah-wadai da binciken Magu
‘Yan jarida ba su samun damar halartar wannan zama da ake yi, don haka ne manema labarai su ka dogara da Lauyoyi wajen samun bayanan zaman.
Jaridar ta ce ana samun labarin wannan bincike ne daga lauyoyi da shaidun da su ka halarci zaman, bayan kiran a fadada masu zuwa zaman ya faskara.
Wasu Lauyoyi biyu da su ka tsayawa tsohon shugaban EFCC, Magu, da su ka halarci zaman mako jiya, sun ce Salami ya na nadamar karbar wannan bincike.
Tosin Ojaoma da Zainab Abiola sun ce Ayo Salami ya fada masu kafin a soma zama cewa ya yi da-na-sanin amincewa da karbar shugabancin kwamitin.
Lauyar Ibrahim Magu ta bada labari: “Duk mun zauna a matsayinmu na Lauyoyi, Alkali Salami (Ayo Salami) ya ce ya yi nadamar aiki a kwamitin nan.”
KU KARANTA: Lauyan Magu ya rubutawa kwamitin Ayo Salami takarda
Ta ke cewa: “Mu na fara zama, Salami ya rika nuna nadama, shi (Salami) ya dauko tsummar goge fuska ya ce ya na cike da-na-sanin karbar wannan aiki.”
Da Abiola ta tambayi Lauyan ko cewa ya na wannan kuka ne a dalilin gaza samun Magu da wani laifi, sai ya cigaba da fadin abin da ya ke fada na nadama.
Shi ma Ojaoma ya ce: “Salami ya yi ta cewa ya ji kunyar karbar wannan aiki. Ya koka da cewa ya yi ritaya, ya na zaune bai da wata damuwa, ya na cin tuwo.”
Ku na da labari cewa Salami da ‘yan kwamitinsa su na binciken aikin da Ibrahim Magu ya yi a EFCC a sakamakon korafin da Abubakar Malami ya gabatar.
Kwamitin Salami, ya nemi a kara masa lokaci domin ya karkare aiki kafin ya mikawa gwamnati
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng