Da duminsa: Saboda yunƙurin shiga yajin aiki, FG da NLC za su gana ƙarfe 7 na dare

Da duminsa: Saboda yunƙurin shiga yajin aiki, FG da NLC za su gana ƙarfe 7 na dare

- Gwamnatin tarayya za ta gana da kungiyar kwadago a yau Lahadi, 27 ga watan Satumba da karfe 7:00 na yamma

- Hakan na daga cikin kokari da gwamnati ke yi na hana kungiyar tafiya jayin aiki kan karin farashin man fetur da kudin wutar lantarki

- Za su gana ne a fadar shugaban kasa da ke babbar birnin tarayya, Abuja

A wani yunkuri na hana tafiya yajin aiki da kungiyar kwadago ke shirin yi, gwamnatin tarayya ta shirya wata ganawa da shugabancin kungiyar da karfe 7:00 na yammacin yau Lahadi, 27 ga watan Satumba.

Da farko an dage ganawar tasu zuwa ranar Litinin da karfe 3:00 na rana biyo bayan rashin cimma matsaya a tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadagon kan karin kudin man fetur da na lantarki.

Mataimakin daraktan labarai da hulda da jama’a, na ma’aikatar kwadago da daukar ma’aikata, Charles Akpan, ya tabbatar da batun ganawar a wani sakon waya.

KU KARANTA KUMA: Mutum 18 aka kashe a harin da aka kai kan motocin gwamnan Borno – Hedkwatar tsaro

Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya za ta gana da kungiyar kwadago a yau Lahadi da karfe 7:00 na yamma
Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya za ta gana da kungiyar kwadago a yau Lahadi da karfe 7:00 na yamma Hoto: @MobilePunch
Source: UGC

Za a yi ganawar ne a dakin taro na Old Banquet Hall da ke fadar Shugaban kasa, Abuja da karfe 7:00 na yamma, jaridar The Nation ta ruwaito..

Sakon ya zo kamar haka: “Mai girma ministan kwadago da daukar ma’aikata, Dr. Chris Ngige zai gana da kungiyar kwadago.

“Taron wanda da farko an shirya yin sa ne a ranar Litinin, 28 ga watan Satumba, a yanzu zai gudana ne kamar haka:

“Rana: Yau, Lahadi, 27 ga watan Satumba 2020.

“Waje: Banquet Hall, fadar Shugaban kasa.

“Lokaci: Karfe 7:00 ma yamma."

KU KARANTA KUMA: Sabon sarkin Zazzau: Na shiga littafi na uku kuma na karshe, inji El-Rufai

A baya mun ji cewa, Gwamnatin Nigeria ta samu sabon umurni daga kotu, na dakatar da kungiyar kwadago daga shiga yajin aikin da suka shirya shiga ranar Litinin.

Mai shari'a Ibrahim Galadima na kotun masana'antu ta kasa, ya bayar da umurnin a Abuja, biyo bayan bukatar hakan da Antoji Janar na kasa ya gabatar gaban kotun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel