Mutum 18 aka kashe a harin da aka kai kan motocin gwamnan Borno – Hedkwatar tsaro

Mutum 18 aka kashe a harin da aka kai kan motocin gwamnan Borno – Hedkwatar tsaro

- Rahoton hedkwatar tsaro ya nuna cewa rayuka 18 aka rasa a harin da Boko Haram suka kai wa ayarin Gwamna Zulum na jihar Borno

- Wadanda suka rasu sun hada da jami’an yan sanda 10, sojoji hudu da yan farar hula hudu

- Tuni rundunar sojin Najeriya ta tura tawagar kwararru a harkar bama-bamai domin tabbatar tantancewa da kakkabe hanyar don gudun sake faruwar haka

Hedkwatar tsaro ta bayyana cewa mutum 18 yan ta’addan Boko Haram suka kashe a wani harin bazata da suka kai kan ayarin motocin gwamnan jihar Borno a ranar Juma’a.

Da yake bayyana hakan a cikin wani jawabi, jagoran labarai na ayyukan tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya ce jami’an yan sanda 10, sojoji hudu da yan farar hula hudu aka kashe a harin da ya afku a kauyen Barwati.

A cewar kakakin sojin, wani abun fashewa da yan ta’addan suka dasa a hanya ne ya halaka mutanen, Channels TV ta ruwaito.

Ya ci gaba da bayyana cewa yan ta’addan sun yi gaba da motocin yan sanda biyu, amma ya kara da cewa dakarun da suka fatattaki yan ta’addan sun yi nasarar kwato motocin sannan suka kwato wata bindigar toka na Boko Haram.

Mutum 18 aka kashe a harin da aka kai kan motocin gwamnan Borno – Hedkwatar tsaro
Mutum 18 aka kashe a harin da aka kai kan motocin gwamnan Borno – Hedkwatar tsaro Hoto: @vanguardngrnews
Source: Twitter

A cewar Enenche, tuni rundunar sojin Najeriya ta tura tawagar kwararru a harkar bama-bamai domin tabbatar tantancewa da kakkabe hanyar don gudun sake faruwar haka.

KU KARANTA KUMA: Sabon sarkin Zazzau: Na shiga littafi na uku kuma na karshe, inji El-Rufai

Ya ce:

Yan ta’addan Boko Haram/ISWAP sun kai hari ga ayarin motocin gwamnatin jihar Borno da suka hada da rundunar sojin Najeriya, rundunar yan sanda da na yan sa kai, a kauyen Barwati a ranar 25 ga watan Satumba, 2020.

“Sai dai dakarun soji sun yi nasarar dakile harin. Amma abun bakin ciki, an rasa rayuka 18 da suka hada da sojoji hudu, yan sanda 10 da yan farar hula hudu.

“Dakarun da suka fatattaki yan ta’addan sun yi nasarar kwato motoci uku.

“Biyu daga cikin motocin ya kasance na rundunar yan sandan Najeriya da yan ta’addan suka sace a yayin harin. Haka zalika an kwato bindigar toka guda daya.

“Rayukan da aka rasa ya kasance sakamakon tashin wasu bama-bamai da yan ta’addan suka dasa.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya jajantawa Zulum bisa harin da 'yan ta'adda suka kai wa tawagarsa a Borno

“Tuni rundunar sojin Najeriya ta tura tawagar warware bama-bamai don suyi aiki kakkaba domin gudun sake faruwar lamarin.”

A gefe guda, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Asabar ya yi Allah wadai ta harin da aka kai wa tawagar gwamnan Borno, Babagana Zulum.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel