Marigayi Mai Deribe: Hotuna da bidiyon gidan zinarin hamshakin mai kudin arewacin Najeriya

Marigayi Mai Deribe: Hotuna da bidiyon gidan zinarin hamshakin mai kudin arewacin Najeriya

- Marigayi Alhaji Mai Deribe yana daya daga cikin hamshakan masu kudin Najeriya da suka mori dukiyarsu kuma har duniya ta dinga sha'awarsu

- Deribe ya gina wata gagagrumar fada a Maiduguri wacce magina suka kwashe shekaru 10 suna aikinita kafin su kammala

- Daga cikin manyan mutane a duniya da fadar ta bai wa masauki akwai tsohon shugaban kasar Amurka, Geroge Bush da Olusegun Obasanjo

Marigayi Alhaji Mai Deribe babu shakka yana daya daga cikin hamshakan masu kudi a Najeriya a shekarun 1980. Ya gina gida wanda aka yi shi da ruwan zinari sannan ya mallaki wani jirgin sama kirar Gulfstream G550.

Kamar yadda Northeast Reporters suka wallafa, yana daya daga cikin mutane 12 da suka taba mallakar irin wannan jirgin saman a fadin duniya.

Marigayi Mai Deribe: Bidiyon gidan zinarin hamshakin mai kudin arewacin Najeriya
Marigayi Mai Deribe: Bidiyon gidan zinarin hamshakin mai kudin arewacin Najeriya. Hoto daga Northernreporters
Asali: UGC

KU KARANTA: Ban taba karbar cin hanci ba a rayuwata, duk wanda ya taba bani ya fito - Magu

Gidansa, wanda ake kira da Gidan Deribe, ya ja hankulan jama'a masu tarin yawa a duniya. Ba abun mamaki bane ganin yadda ya dinga saukar manyan mutane a duniya kamar Yarima Charles da matarsa, marigayiya Gimbiya Diana.

Marigayi Mai Deribe: Bidiyon gidan zinarin hamshakin mai kudin arewacin Najeriya
Marigayi Mai Deribe: Bidiyon gidan zinarin hamshakin mai kudin arewacin Najeriya. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

Sauran wadanda suka taba shiga Gidan Deribe akwai tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Sarki Juan Carlos na kasar Spain da tsohon shugaban kasar Amurka, George Bush.

Shugaban kasar mulkin soja na wancan lokacin, Janar Ibrahim Babangida, shi ya jagoranci bude fadar zinarin bayan kammala ginin da aka yi.

Marigayi Mai Deribe: Bidiyon gidan zinarin hamshakin mai kudin arewacin Najeriya
Marigayi Mai Deribe: Bidiyon gidan zinarin hamshakin mai kudin arewacin Najeriya. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

An gano cewa, an kashe dala miliyan 100 a wancan lokacin wurin ginin yayin da gyaran gidan a kowanne wata yake lamushe dala miliyan biyar.

Mutumin ya kwashe shekaru 12 kacal bayan gama ginin kafin ya rasu. An gano cewa, gidan yana da sassa daban-daban wanda ya baiwa kowacce matarsa daya.

Dansa, Shettima Abubakar Deribe, ya tabbatar da cewa an dinga aikin gidan na shekaru 10 babu tsaywa kafin a kammala.

Shettima ya tabbatar da cewa, harsashi baya iya bula kofar gidansu.

An haifa marigayin a 1924 kuma ya rasu a 2002 a Makka, kasar Saudi Arabia. Ya rasu ya bar 'ya'ya 27.

KU KARANTA: Bidiyon karamar yarinya tana bai wa iyayenta shawara a kan aure ya janyo cece-kuce

A wanii labari na daban, a kowacce jiha a Najeriya, ba'a rasa masallatai masu kyau. Musulumci yana daya daga cikin manyan addinai da mutanen Najeriya har da Afirika sukayi imani da shi.

Musulunci ba addini kadai ya shafa ba, hatta gine-ginen Afirika ya shafa. Ana samun Masallatai masu kyau a kowacce jiha a kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel