Boko Haram: Dakarun Gwamnan Jihar Borno da aka rasa za su haura 20

Boko Haram: Dakarun Gwamnan Jihar Borno da aka rasa za su haura 20

- Wadanda su ka mutu a harin da aka kai wa Gwamnan Borno sun kara yawa

- Adadin wadanda su ka ransu a sanadiyyar wannan hari za su haura 30 yanzu

- Ana zargin Sojojin ISWAP ne su ka kai wa tawagar Umar Zulum hari a Baga

A ranar Asabar mu ka samu labari cewa yawan jami’an tsaron da su ka mutu a harin da aka kai wa Gwamna Babagana Umara Zulum sun karu.

Wata majiya ta shaidawa gidan yada labarai na AFP cewa adadin gawawwakin da aka samu bayan an kai wa gwamnan Borno hari ta kara yawa.

Majiyar ta shaidawa manema labarai cewa an samu akalla gawawwaki 30 daga tawagar gwamnan.

Gawawwakin da aka samu sun hada da na jami’an ‘yan sanda 12, sojojin kasa biyar, da kuma wasu hudu daga cikin dakarun sa-kai watau C-JTF.

KU KARANTA: Sojoji sun binciki harin da aka kai wa Babagana Zulum

Har ila yau an samu karin mutane tara masu fararen kaya da su ka mutu a dalilin wannan mummunan hari da aka kai a ranar Juma’a.

“Adadin wadanda aka tabbatar sun mutu sun karu zuwa 30 domin an dauki gawan mutane daga baya a yankin bayan an kai wannan harin.”

Majiyar ta kuma shaidawa manema labarai a ranar Asabar cewa an yi wa mutane da-dama rauni.

Wani jami’in tsaro da ya tattauna da AFP ya tabbatar da hakan, ya ce wadanda su ka rasa ransu a wannan hari na yammacin Juma’a sun kai akalla 30.

Boko Haram: Dakarun Gwamnan Jihar Borno da aka rasa za su haura 20
Gwamnan Jihar Borno a IDP Hoto: Guardian
Asali: UGC

KU KARANTA: Farfesa Zulum ya nada Sarki a Biu

Wannan jami’i ya kuma yi karin bayani, ya ce ‘yan ta’addan sun yi nasarar karbe motoci takwas daga tawagar da ta ke tare da Gwamna Umara Zulum.

Ya ce: “’Yan ta’addan sun tsere da motar bindiga, da igwa-igwa da kuma kananan motoci shida.”

A jawabin da ‘yan sandan Najeriya su ka fitar, sun tabbatar da cewa ‘Yan ta'adda da ake zargin 'yan kungiyar ISWAP ne su ka kai wa gwamnan hari.

Sojojin ISWAP sun afkawa tawagar Babagana Zulum ne a yankin Baga da ke kusa da tafkin Chadi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng