Jihar Bauchi ta tsayar da ranar bude makarantu a cikin watan Oktoba

Jihar Bauchi ta tsayar da ranar bude makarantu a cikin watan Oktoba

- Har yanzu makarantu ba su koma bakin aiki ba tun bayan rufesu sakamakon barkewar annobar korona

- Gwamnatin tarayya ta bawa gwamnatocin izinin bude makarantu matukar za su yi biyayya ga dokoki da shawarwarin hukumar NCDC da ma'aikatar lafiya

- Bayan hakan ne wasu jihohi su ka fara saka ranakun da za su bude makarantunsu domin dalibai su koma aji

Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da cewa za ta bude makarantun Sakandire daga ranar 12 ga watan Oktoba mai kamawa.

Kwamishinan ilimi a jihar Bauchi, Dakta Aliyu Tilde, ne ya sanar da hakan ranar Juma'a, 25 ga watan Satumba.

Ya ce sun amince da bude makarantun ne bayan kammala wani taro na kwamishinonin ilimi daga jihohin arewa 19 wanda aka yi a Abuja.

Yayin taron, an amince cewa jihohi za su bude makarantun sakandire kafin zuwa ranar 30 ga watan Oktoba.

DUBA WANNAN: Asiri ya tonu: An bankado kamfanin da ke sarrafa kororon robar da aka riga akayi amfani da su

Dakta Tilde ya kara da cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya amince da ranar bude makarantun tun ranar 23 ga watan Satumba.

Jihar Bauchi ta tsayar da ranar bude makarantu a cikin watan Oktoba
Bala Mohammed
Asali: UGC

"Ana bukatar dukkan malamai da sauran ma su taimaka musu a makarantu su koma bakin aiki daga ranar 3 ga watan Oktoba domin fara shirye-shiryen dawowar dalibai kamar yadda gwamnati ta amince," a cewar Dakta Tilde.

Kwamishinan ya kara da cewa umarnin bude makarantun bai shafi manyan makarantun gaba da sakandire ba saboda suna da tsarinsu daban.

DUBA WANNAN: Zafafan hotunan auren Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Buhari

Bayan kara wa'adin sassauta dokar kulle a fadin Najeriya, gwamnatin tarayya ta bawa jihohi izinin bude makarantun sakandire bisa biyayya ga tsari da shawarwarin ma'aikatar lafiya da hukumar NCDC.

Jihohi da dama, musamman a kudancin Najeriya, sun sanar da ranakun bude makarantunsu na sakandire bayan samun izinin gwamnatin tarayya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel