Yadda aka kashe jami'in DSS a Plateau

Yadda aka kashe jami'in DSS a Plateau

- Hukumar 'yan sandan farin kaya, DSS, ta rasa wani jami'inta mai suna Mukhtar Modibbo dan asalin garin Misau a jihar Bauchi

- Jami'in ya rasa ransa ne sakamakon harbinsa da aka yi yayin wata sumame da jami'an tsaro suka kai mabuyar dilalan bindiga a karamar hukumar Shendam a jihar Plateau

- Jami'an tsaron na hadin gwiwa da suka kunshi sojoji da DSS sun kai sumamen ne bayan samun bayanan sirri cewa dilalan bindigan na da mabuya a kauyen

An kashe jami'in hukumar 'yan sandan farin kaya, DSS, a daren ranar Laraba yayin musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da dilalan bindiga a kauyen Kalong da ke karamar hukumar Shendam ta jihar Plateau.

Daily Trust ta ruwaito cewa sunan jami'in da aka kashe Barista Mukhtar Moddibo dan asalin karamar hukumar Misau daga jihar Bauchi.

Yadda aka kashe jami'in DSS a Plateau
Yadda aka kashe jami'in DSS a Plateau. Hoto @channelstv
Source: Twitter

DUBA WANNAN: APC ta dakatar da hadimin Buhari, surukin Tinubu da wasu mutane takwas

An kai gawar Moddibo asibitin koyarwa ta Jami'ar Jos (JUTH).

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin wani sumame na hadin gwiwa tare da sojojin Najeriya a kauyen inda aka harbi Moddibo yayin musayar wuta da jami'an tsaron suka yi da dilalan bindigan.

Jami'an tsaron ciki har da DSS sun kai sumame ne a kauyen domin kama shugaban dilalan bindigu da wasu masu safarar makamai bayan samun bayanan sirri cewa suna boye a kauyen.

An tattaro cewa jami'an na DSS sun kama wasu dilalan bindiga dauke da AK 47 guda biyar kafin afkuwar lamarin.

KU KARANTA: Borno: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin 'yan Boko Haram 7 a Tafkin Chadi

Lamarin ya faru ne a lokacin da jami'an na DSS ke kokarin kamo masu garkuwa, 'yan bindiga da masu safarar bindigu da ke adabar sassa daban-daban a jihar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa jami'an tsaron sunyi nasarar kama wanda ya kashe lakcara a jami'ar Jos mai suna Dakta Joanna Drenkat wanda masu garkuwa suka kashe.

Shugaban Kungiyar Yarabawa ta Yoruba World Congress, Farfesa Banji Akintoye ya ce ƙungiyar za ta kafa ƙasar Yarabawa ta tare da zub da jini ba.

Ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba yayin bikin tunawa da Yaƙin Kirji kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel