Ganduje ya amince da nadin manyan sakatarori 4 a jihar Kano (jerin sunaye)

Ganduje ya amince da nadin manyan sakatarori 4 a jihar Kano (jerin sunaye)

- Gwamnatin Kano ta nada manyan sakatarori hudu a ma'aikatun gwamnatin jihar

- Wadanda aka nada sune Fatima Fulani Sarki Sumaila, Umar Liman Albasu, Kabiru Sa’idu Magami da kuma Abba Mustapha Dambatta

- Gwamna Ganduje ya yi kira a garesu da su zamo masu ‘kwazo da jajircewa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da nadin manyan sakatarori hudu a ma'aikatun gwamnatin jihar.

Ganduje ya yi kira ga manyan jami’an gwamnatin da aka nada da su zamo masu ‘kwazo da jajircewa wajen sauke hakokin da ya rataya a wuyansu.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na gwamnatin jihar, Abba Anwar, ya fitar a ranar Alhamis, 24 ga watan Satumba.

Jawabin yi kira a gare su da su inganta ayyukansu, inda ya jaddada cewa, “dole ne ku bi ka’idoji masu nagarta irin na manyan kasashen duniya a matsayinku na manyan jami’an gwamnati a jihar”.

KU KARANTA KUMA: Ba Kanal Baƙo kaɗai aka kashe ba: Dakarun soji sun nuna fushi kan ware sauran sojoji

Ganduje ya amince da nadin manyan sakatarori 4 a jihar Kano (jerin sunaye)
Ganduje ya amince da nadin manyan sakatarori 4 a jihar Kano (jerin sunaye) Hoto: @ImamShams
Asali: Twitter

Sakatarorin da aka nada sune; Fatima Fulani Sarki Sumaila, Umar Liman Albasu, Kabiru Sa’idu Magami da kuma Abba Mustapha Dambatta.

KU KARANTA KUMA: Wannan shine shan shayina na karshe a matsayin gwauro - Bashir Ahmad

Sanarwar ta ce gwamnan na umartar sabbin manyan sakatarorin da su kara himma da kiyaye mutuncin aikinsu.

Har ila yau ya kuma horesu da su kasance abin koyi ga sauran kananan ma’aikatan gwamnatin masu tasowa.

A gefe guda, Legit.ng ta kawo cewa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da muhimman shawarwari a kan yadda za a kawo karshen kalubalen matsalar tsaro.

A cewar Ganduje, gwamnati za ta iya shawo kan matsalar tabarbarewar tsaro ta hanyar amfani da sabon ilimin fasahar sarrafa bayanai (ICT), amfani da 'yan sandan cikin al'umma da kuma hada gwuiwa tsakanin hukumomin tsaro.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel