Murnar zagayowar ranar samun 'yanci: Hotunan shugaba Buhari a Bissau

Murnar zagayowar ranar samun 'yanci: Hotunan shugaba Buhari a Bissau

- Shugabannin kasashen nahiyar Afrika sun halarci taron bikin taya kasar Guinea-Bissau murnar cika shekaru 47 da samun 'yanci

- Wannan shine karo na farko da shugaba Buhari ya ziyarci kasar Guinea-Bissau tun bayan hawansa mulki a shekarar 2015

- A cikin jawabin da ya gabatar, shugaba Buhari ya dauki alkawarin cewa Najeriya za ta tallafawa kasar Guinea-Bissau ta hanyoyi da dama

A yau, Alhamis, ne kasar Guinea Bissau ta ke murnar cika shekaru 47 da samun 'yancin kai.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya na daga cikin shugabannin kasashen nahiyar Afrika da su ka ziyarci kasar Guinea domin tayasu murnar zagayowar ranar da su ka samu 'yanci.

Da ya ke gabatar da jawabi yayin taron, shugaba Buhari ya dauki alkawarin cewa Najeriya za ta tallafawa kasar Buinea-Bissau ta hanyoyi da dama tare da bayyana cewa; "ribar nahiyar Afrika ta yamma ce idan aka samu zaman lafiya da cigaba a Guine-Bissau."

Femi Adesina ya rawaito Buhari ya na cewa ya ji dadin karramashi da aka yi a Guinea-Bissau musamman kasancewar wannan ita ce ziyararsa ta farko zuwa kasar tun bayan hawansa mulki a shekarar 2015.

KARANTA: Yajin aikin NLC: Gwamnoni za su gudanar da taron gaggawa ranar Alhamis

Tun a jiya, Laraba, Legit.ng ta wallafa labarin cewa shugaba Muhammadu Buhari zai yi tafiya kasar Guinea Bissau daga birnin tarayya Abuja ranar Alhamis, 23 ga Satumba halartan taron murnar shekaru 47 da samun yancin kasar.

Murnar zagayowar ranar samun 'yanci: Hotunan shugaba Buhari a Bissau
Buhari a Bissau
Asali: Twitter

Mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ne ya sanar da hakan a shafin fadar shugaban kasa na manhajar Facebook.

Ya bayyana cewa shugaban kasan zai hadu da takwarorinsa na kasan Cote d’ Ivoire, Rwanda, Mauritania, Togo da Liberia.

Yace: "A birnin Bissau, shugaba Buhari zai kaddamar da sabuwar titin da aka sanyawa sunansa domin karramashi."

KARANTA: Yadda za a kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya - Ganduje ya bawa FG satar amsa

"Bayan haka shugaban kasan da sauran shugabannin kasashen da aka gayyata zasu halarci liyafar da shugaban Guinea Bissau, Umaru Sissoco Embalo, ya shirya."

"Shugaban kasan zai samu rakiyar manyan jami'an gwamnati wanda ya hada da ministan harkokin waje, Geofrey Onyeama; ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (Mai ritaya); mai bada shawara kan tsaron kasa, Babagana Monguno; da dirakta Janar na hukumar NIA, Ahmed Rufai Abubakar."

A karshe, Adesina ya bayyana cewa shugaban kasa zai dawo Najeriya ana kammala taron.

Murnar zagayowar ranar samun 'yanci: Hotunan shugaba Buhari a Bissau
Buhari a Bissau
Asali: Twitter

Murnar zagayowar ranar samun 'yanci: Hotunan shugaba Buhari a Bissau
Shugaba Buhari a Bissau
Asali: Twitter

Murnar zagayowar ranar samun 'yanci: Hotunan shugaba Buhari a Bissau
Shugaba Buhari a Bissau
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng