Jerin masu halin da su ka koma ba su da dukiya a Duniya da labaransu

Jerin masu halin da su ka koma ba su da dukiya a Duniya da labaransu

- Duniya ta taba yin hamshakan masu kudin da su ka dawo ba su da komai

- Wasu daga cikinsu sai da ta zama ba su da taro, wasu kuma sai tulin bashi

- Irinsu Bernie Madoff, Allen Stanford, da Eike Batist su na tsare a kurkuku

Jaridar Business Insider ta tattaro jerin wasu tsofaffin shahararrun attajirai goma da yanzu su ka koma abin tausayi. An kawo takaitaccen labarin yadda su ka tsiyace:

1. Patricia Kluge

Patricia Kluge ta samu dukiya bayan ta rabu da attajirin mijinta, amma daga baya ta koma tutar babu a lokacin da hannun jarin masu harkar saida gidaje ya kife war-was.

2. Vijay Mallya

Mallya ya samu kan shi a matsala ne a sakamakon katutun bashin banki. Yanzu haka hukumomin Indiya su na neman yadda za su kama tsohon mai kamfanin jiragen.

KU KARANTA: Matashin da Amurka ta ke nema ya sallama kansa a Legas

3. Sean Quinn

An yi lokacin da duk kasar Ireland, babu atttajiri irin Sean Quinn. A karshe ‘dan kasuwar ya rasa duk dukiyarsa, kusan Dala biliyan 2.8, ta koma bai da komai a asusu sai $50, 000.

4. Jocelyn Wildenstein

Shekarun baya Jocelyn Wildenstein ta taba batar da Dala miliyan $1 wajen facaka a cikin wata guda. A 2018, wannan Baiwar Allah ta wayi gari ba ta da sisin kobo ko dalilinsu.

5. Bernard Madoff

Ana yi wa Bernard "Bernie" Madoff da lakabi da Sarkin ‘Yan Ponzi. A dalilin damfararsa, aka daure gawuraccen attajiirin a Amurka, zai shafe shekara 150 a gidan kurkuku.

6. Elizabeth Holmes

Akwai lokacin da Elizabeth Holmes ta ba Dala biliyan biyar baya. Daga baya aka gano rashin gaskiya a kamfaninta na Therenos. Yanzu haka babu abin da ya ragewa Holmes.

Jerin masu halin da su ka koma ba su da dukiya a Duniya da labaransu
Allen Stamford ya na kurkuku yanzu Hoto: Business Insider
Source: UGC

KU KARANTA: Hamshakan Attajiran Najeriya da su ka fito daga Arewa

7. Björgólfur Gudmundsson

Rugujewar babban bankin Landsbanki ne ya karya attajirin kasar Iceland, Gudmundsson. Tun shekaru fiye da goma da su ka wuce wannan Bawan Allah ya zama bai da ko anini.

8. Allen Stanford

Daga cikin masu zaman gidan kurkuku cikin tsofaffin Attajiran da aka yi akwai Allen Stanford. Shi ma an kama shi ne da laifin damfarar Bayin Allah, zai yi shekaru 110 a daure.

9. Eike Batista

A shekarar 2013 kamfanin Eike Batista na OGX ya tsiyace. Daga baya kuma aka yankewa tsohon Attajirin daurin shekaru 30 bayan an same shi da laifin bada rashawa a kasar Brazil.

10. Donald Trump

Ko da shugaban kasar Amurka, Donald Trump bai taba tsiyacewa ba, kamfanoninsa da yawa sun tsiyace, ana zargin akalla kamfanoni shida na shaharraen mai kudin sun mutu yanzu.

Idan za ku tuna a shekarar 2017 ne mujallar Forbes fitar da jerin sunayen jiga-jigan matasa ‘yan kasuwa 30 masu kasa da shekara 30 da haihuwa, da su ke juya kasashen Duniya.

A cikin wannan jeri an samu sunayen mutane har biyar da su ka fito daga Najeriya

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel