Abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da sabon sarkin Biu Mai Mustapha Umar

Abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da sabon sarkin Biu Mai Mustapha Umar

- An nada Alhai Mai Mustapha Umar a matsayin sabon sarkin Biu

- Mai Mustapha babban da ne ga marigayi tsohon sarkin Biu, Mai Umar Mustapha Aliyu

- Kananan hukumomin Biu, Bayo, Kusar da kuma Kwaya duk suna a karkashin Biu ne

Bayan rasuwar sarkin Biu, an nada babban dansa domin ya gaje sa, Alhaji Mai Mustapha Umar domin ya gaji mahaifinsa.

Zuwa yanzu dai masarautar na ci gaba da karbar gaisuwar caffa ga sabon sarkin yayinda ake ci gaba da jimamin rasuwar tsohon sarkin.

Don haka muka kawo maku wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da sabon sarkin.

KU KARANTA KUMA: Wannan shine shan shayina na karshe a matsayin gwauro - Bashir Ahmad

1. Haihuwa

An haifi sabon sarkin Biu, Mai Mustapha Umar a ranar 20, ga watan Yuli, 1970.

Mai Mustapha ya kasance babban dan marigayi sarkin Biu, Mai Mustapha Aliyu. Yanzu haka yana da shekaru 50 a duniya.

Abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da sabon sarkin Bi’u, Mai Mustapha Umar
Abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da sabon sarkin Bi’u, Mai Mustapha Umar Hoto: Governor of Borno
Source: Facebook

2. Karatu

Sabon sarkin ya yi karatunsa na firamare a makarantar Biu Central Primary School daga 1975 zuwa 1981.

Bayan nan sai ya tafi makarantar sakandare na gwamnati da ke Biu a1983 ya kuma kammala a 1989.

Ya yi karatun difloma a kan gudanar da ayyukan kananan hukumomi a kwalejin CAPS da ke Potiskum tsakanin 1995 zuwa 1996.

Daga shekarar 2010 zuwa 2015, sabon sarkin ya koma karatu, inda ya karanci ilimin kasuwanci a jami’ar Maiduguri.

3. Aiki

Sabon sarkin ya fara aiki a matsayin matsayin mataimakin akawu a sashen harkukin kudi na karamar hukumar Bi’u a shekarar 1988, bayan nan sai aka nada shi a matsayin dakacin sabuwar yanki da aka kafa na Biu maso yamma a 1999.

An kuma nada Mustaba sarautar Midalan Biu a watan Maris din shekarar 2016.

KU KARANTA KUMA: Babbar magana: Likitoci sun kasa gano dalilin da ya sa ƴar shekara 15 ke kukan jini

4. Masarautar Bi’u

An nada shi sarkin Biu na 29 a ranar Talata, 22 ga watan Satumba, bayan rasuwar mahaifinsa, Mai Mustapha Aliyu wanda ya rasu sakamakon rashin lafiya.

Kananan hukumomin da ke karkashin masarautar mai daraja ta daya sun hada da Biu, Bayo, Kusar da kuma Kwaya.

A gefe guda, mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jimamin mutuwar Sarakunan Borno guda biyu - Shehun Bama, Shehu Kyari Ibn Umar El-Kanemi da Sarkin Biu Mai Umar Mustapha Aliyu.

A cewarsa, mutuwar Sarakunan guda biyu a lokaci daya, duka biyu ne mai wuyar shanyewa, kuma dole 'yan Nigeria su ji radadin mutuwar Sarakunan biyu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel