Na yi alƙawarin COVID-19 ba za ta kashe kowa a Taraba ba - Gwamna Ishaku

Na yi alƙawarin COVID-19 ba za ta kashe kowa a Taraba ba - Gwamna Ishaku

- Gwamna Darius Ishaku na Taraba ya dauki alkawarin cewa babu wanda cutar korona za ta kashe a jiharsa

- Ishaku ya bayyana irin tanadin da gwamnatinsa ta yi domin fatattakar cutar daga cikin jihar gaba daya

- Ya kuma jinjina wa kwamitin korona a jihar kan namijin kokarin da suke yi don daidaita lamarin

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, a ranar Talata, ya ce gwamnatinsa na iya bakin kokarinta don tabbatar da babu wanda ya mutu sakamakon cutar korona a jihar.

Ishaku ya ce gwamnatinsa na fadada cibiyoyin gwaji da na killace masu cutar a jihar domin tabbatar da ganin an kula da lamuran COVID-19 yadda ya kamata a jihar.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da mambobin kwamitin korona a jihar karkashin jagorancin shugabansu, Dr Innocent Vakkai, suka gabatar masa da rahoto na ayyukan kwamiti a gidan gwamnati, Jalingo, a ranar Talata.

KU KARANTA KUMA: Uzodinma: Ka yi shiru, ba ka nan lokacin da ake gwagarmaya a APC inji Kawu Sumaila

Ishaku ya fada ma kwamitin cewa gwamnatinsa na bunkasa cibiyoyin gwaji da na kula da masu cutar a jihar domin shirya wa sashi na gaba a yaki da take da annobar.

Gwamnan, wanda ya alakanta karancin masu cutar da ake samu da yawan masu warkewa daga cutar da ake samu a jihar da irin shirin da gwamnatinsa tayi, ya yi kira ga jama’ar jihar da su ci gaba da bin dokokin COVID-19.

Na yi alƙawarin COVID-19 ba za ta kashe kowa a Taraba ba - Gwamna Ishaku
Na yi alƙawarin COVID-19 ba za ta kashe kowa a Taraba ba - Gwamna Ishaku Hoto: @tarabagovt
Asali: Twitter

"Ana kokari don ganin an fatattaki cutar gaba daya daga jihar Taraba da kuma tabbatar da cewar babu wanda ya mutu sakamakon cutar.

“Gwamnatina na bunkasa cibiyoyin gwaji da na killace masu cutar a jihar don tabbatar da kula da lamarin yadda ya kamata a jihar.

“Ina jinjina ga mambobin kwamitin a kan namijin kokari da suka yi kuma zan ci gaba da basu goyon baya domin su yi fiye da haka,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: Jam'iyyar NCP ta buƙaci a soke zaɓe, a hukunta Obaseki

An samu mutum 95 da suka kamu da cutar a Taraba sannan babu wanda ya mutu zuwa yanzu, jaridar Punch ta ruwaito.

A gefe, hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 176 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Talata 22 ga Satumba, shekarar 2020.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel