Borno: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin 'yan Boko Haram 7 a Tafkin Chadi
- Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewa ta kashe manyan kwamandojin ƴan ta'adda a yayin wasu hare-hare da ta kai a Tafkin Chadi
- Kwamandojin ƴan ta'addan da aka kashe sun hada da Abu Usman, Alhaji Shettima, Modu Mainok, Bukar Gana, Abu Summayya, Amir Taam da Amir Kuraish
- Rundunar sojojin ta yi kira ga mutanen yankin su cigaba da taimakawa rundunar da bayyanan sirri da haɗin kai
DUBA WANNAN: An huro wa tsohon minista wuta kan zarginsa da bada umurnin yi wa ma'aikatansa zigidir saboda N5,000
A cigaba da ayyukan ta na kawo ƙarshen ta'addanci a arewa maso gabas, dakarun soji na Super Army Camp da ke Camp Malumfatori a Tafkin Chadi ta samu nasara a wasu sumame da ta kai.
An yi nasarar gano sansani da maɓuyar ƴan ta'adda a Tunbun Gini, Tunbun Nbororo, Tunbun Kayoma, Tunbun Kaza da Tunbun Fulani a Tafkin Chadi a ƙaramar hukumar Kukawa na jihar Borno.
Sojojin sun yi nasarar kashe manyan kwamandojin ƴan ta'adda cikin su har da Abu Usman, Alhaji Shettima, Modu Mainok, Bukar Gana, Abu Summayya, Amir Taam da Amir Kuraish a yayin sumamen.
KU KARANTA: Dalilin da yasa 'yan Najeriya ke korafi kan karin kudin wutar lantarki - Sanusi II
Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin Kakakin hedkwatar tsaro, Manjo Janar John Enenche da ya fitar a shafin hukumar da ke Twitter.
Sanarwar ta cigaba da cewa rundunar sojin da sauran hukumomin tsaro za su cigaba da aiki don kawo ƙarshen ta'addanci da sauran ƙallubalen tsaro a kasar.
Enenche ya tabbatar wa al'ummar yankin cewa rundunar soji ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin sauke nauyin da ya rataya a wuyan ta na tsare rayuka da duniyoyin al'umma.
Ya kuma yi kira ga al'ummar yankin su cigaba da taimakawa rundunar da bayannan sirri masu amfani.
A wani rahoton daban, mahalarta wani taron rana guda da aka yi a ranar Litinin a Katsina sun bukaci mazauna jihar su rika kare kansu duk lokacin da 'yan bindiga ko wasu miyagu suka kai musu hari.
Sun roki mutane su dena bari sai aikin samar da tsaro a hannun jami'an tsaro su kadai kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng