Moji Ladeji: Buhari ya yi wa tsohon Gwamna Fayose gaisuwar mutuwa

Moji Ladeji: Buhari ya yi wa tsohon Gwamna Fayose gaisuwar mutuwa

- Kwanan nan ne wata ‘Yaruwar tsohon Gwamnan Ekiti, Ayo Fayose ta rasu

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa Ayodele Fayose ta’aziyya jiya

- Ta bakin Femi Adesina, Buhari ya ce mutuwar Moji Ladeji ta fado kwatsam

Mai girma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aika sakon gaisuwar ta’aziyyarsa ga Ayodele Peter Fayose, bayan ya rasa ‘yaruwarsa.

A makon nan ne aka ji cewa babbar yayar tsohon gwamnan Ekiti, Moji Ladeji ta rasu.

A ranar 23 ga watan Satumba, 2020, shugaban kasan ya fitar da gajeren jawabi ya na mai yi wa Ayodele Fayose ta’aziyyar wannan rashi da aka yi masu.

KU KARANTA: Matar da Ministan Buhari ya sallama daga ofis ta samu aiki a Turai

Muhammadu Buhari ya yi addu’a Ubangiji ya ba Fayose hakurin jure rashin ‘yaruwar ta sa. Jawabin ya fito ne daga bakin hadiminsa, Femi Adesina.

Har ila yau, a sakon gaisuwarsa na ranar Laraba, shugaba Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyya ta musamman ga sauran ‘yanuwa da abokan marigayiyar.

Shugaban kasan ya bayyana mutuwar wannan Baiwar Allah da cewa ya zo kwatsam ba tare da shiri ba.

Buhari ya yi kira ga masoya da na-kusa da Marigayiya Moji Ladeji su yi hakuri domin kuwa duk mai rai mamaci ne, ya yi kira da a rungumi kaddarar rashin.

KU KARANTA: Lokacin da Fayose yayi gigin takara da Buhari a zaben 2019

Moji Ladeji: Buhari ya yi wa tsohon Gwamna Fayose gaisuwar mutuwa
Tsohon Gwamna Fayose Hoto: Channels TV
Asali: UGC

A karshe Buhari ya yi wa wanda ta riga mu gidan gaskiyar addu’ar mutuwa ta zama mata hutu.

Moji Ladeji ta rasu ne bayan ta yi fama da gajerar lafiya a farkon makon nan. Fayose wanda shi ya ke bi ma ta a dakinsu, ya sanar da rasuwar a madadin danginsu.

Kwanaki kun ji cewa tsohon gwamna Ayodele Fayose ya ce ya yarda da Olusegun Obasanjo na cewa da ya yi Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta gaza.

Fayose ya ce duk da irin sabani da banbancinsa da tsohon Shugaban kasar, a nan ya yi gaskiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel