Yajin aikin NLC: Gwamnoni za su gudanar da taron gaggawa ranar Alhamis

Yajin aikin NLC: Gwamnoni za su gudanar da taron gaggawa ranar Alhamis

- Har yanzu 'yan Najeriya ba su daina jin zafin karin farashin litar man fetur da gwamnatin tarayya ta yi ba

- Kungiyar Kwadago ta kasa (NLC) ta ce za ta shiga yajin aiki matukar gwamnati ba ta janye karin farashin litar mai da kudin kantarki ba

- A yayin da wa'adin sati biyu da NLC ta bawa gwanati ke dab da cika, kungiyar gwamnoni (NGF) ta kira taron gaggawa

Gwamnonin jihohi 36 da ke Najeriya za su gudanar da taron gaggawa ranar Alhamis domin tattauna yadda za a samu mafita tare da kaucewa shiga yajin aiki da kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ke shirin farawa.

Kungiyar NLC ta bayyana cewa babu gudu, babu ja da baya, a kan niyyarta ta shiga yajin aiki matukar gwamnati ba ta janye karin kudin man fetur da na wutar lantarki ba.

A cikin wata takaitacciyar sanarwa da ta fito daga ofishin shugaban sashen sadarwa da hulda da jama'a na kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), Abdulrazaq Bello Barkindo, an bayyana cewa za a yi taron ne ranar Alhamis a Abuja.

DUBA WANNAN: Kotu ta raba auren shekara uku saboda katsalandan din surukai a rayuwar ma'aurata

A cewar sanarwar, wacce Barkindo ya fitar da yammacin ranar Laraba, za a gudanar da taron ne ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo mai nuna bidiyo da dauko sauti.

Yajin aikin NLC: Gwamnoni za su gudanar da taron gaggawa ranar Alhamis
Kayode Fayemi; Shugaban NGF Tuwita - @kfayemi
Source: Twitter

"Kungiyar gwamnoni ta kira taron gaggawa sakamakon baraxzanar shiga yajin aiki da kungiyar NLC ke yi wa gwamnatin tarayya a kan tashin farashin man fetur da wutar lantarki.

"Dukkan gwamnonin jihohi 36 za su halarci taron domin tattauna yadda za a yi sulhu tare da samun maslaha domin kaucewa fadawa yajin aikin.

DUBA WANNAN: Buhari zai gina layin dogo tun daga Kano har zuwa jamhuriyar Nijar

"Ana saka ran cewa dukkan gwamnoni za su halarci taron saboda za a tattauna muhimman abubuwa da suka shafi kasa domin gudun dagulewar al'amura yayin da ake farfadowa daga tsananin da aka shiga sakamakon bullar annobar korona.

"Za a fara taron, wanda shine irinsa na farko da NGF za ta yi, da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Alhamis, 25 ga watan Satumba," a cewar sanarwar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel