Na damu matuka – Buhari ya yi alhinin mutanen da suka mutu a fashewar tankar fetur a Kogi

Na damu matuka – Buhari ya yi alhinin mutanen da suka mutu a fashewar tankar fetur a Kogi

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jimamin mutuwar mutanen da gobarar tankar Kogi ta cika da su

- A kalla mutum 23 ne suka rasa rayukansu a ranar Laraba, 23 ga watan Satumba, a fashewar tankar mai

- Shugaban kasar ya yi ta’aziyya ga iyalan wadanda suka mutun da gwamnatin jihar Kogi

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna bakin ciki a kan mutuwar mutum 23 wadanda suka rasa rayukansu a ranar Laraba, 23 ga watan Satumba, a fashewar tankar fetur.

Legit.ng ta tattaro cewa da yake martani kan mutuwar wanda hukumar hana afkuwar hatsarurruka ta tarayya ta tabbatar, Buhari ya bayyana lamarin a matsayin cikin abun damuwa da bakin ciki.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Garba Shehu, babban mai ba Shugaban kasar shawara a kafofin watsa labarai.

Buhari ya kuma bayyana cewa ya damu matuka da yawan afkuwar lamura marasa dadi da ke haddasa mace-mace a Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Daga karshe: An nada sabon Sarkin Musawan Katsina

Na damu matuka – Buhari ya yi alhinin mutanen da suka mutu a fashewar tankar fetur a Kogi
Na damu matuka – Buhari ya yi alhinin mutanen da suka mutu a fashewar tankar fetur a Kogi Hoto: Femi Adesina
Source: Facebook

Ya ce: “Na damu sosai game da yawan afkuwar lamura marasa dadi da bakin ciki a kasar wanda ke hadda mace-mace.”

“Wadannan lamura da ke yawan afkuwa wanda ke kai ga rasa rayuka da dukiyoyi kasar sun kasance sakamakon ayyukanmu na rashin bin matakan kariya.”

“Kasarmu ta kasance inda muke ci gaba da rayuwarmu a duk lokacin da mummunan lamari ya afku maimaikon daukar matakan kare kai daga sake afkuwa annobar a gaba.”

Shugaba Buhari ya bayyana cewa da ana bin matakan da aka tanada yaddda ya kamata, toh da an hana afkuwar hatsarurruka da dama.

Yayinda yake jaje ga gwamnatin jihar Kogi da iyalan wadanda suka mutu, shugaba Buhari ya yi kira ga hukumomin da suka kamata da su tashi tsaye.

KU KARANTA KUMA: Yadda za a kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya - Ganduje ya bawa FG shawara

Sannan ya bukaci da su tabbatar da daukar matakan kariya da muhimmanci.

A baya, mun kawo cewa dalibai biyar daga kwalejin Kogi (KSP) Lokoja, da kananan yara uku, tare da wasu mutane 15 suka mutu , sakamakon fashewar tankar man fetur a Lokoja.

Jaridar Tribune Online ta ruwaito cewa tankar man ta afkawa wasu motocin a Felele da ke hanyar Lokoja-Abuja, da misalin karfe 8:30am, yayin da wasu motocin ke fada mata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel