Da duminsa: Kotu ta ƙalubalanci Buhari kan miƙa sunayen lauyoyi 11 don mayar da su masu shari'a

Da duminsa: Kotu ta ƙalubalanci Buhari kan miƙa sunayen lauyoyi 11 don mayar da su masu shari'a

- Wata babbar kotun tarayya ta kalubalanci shugaban kasa buhari a kan mika sanayen lauyoyi 11 majalisa

- Buhari ya mika sunayen lauyoyin domin a tantance su sannan a maishe su alkalai bisa shawarar majalisar alkalai ta kasa

- Sai dai kotun ta ce ba hurumin shugaban kasar bane aikata hakan

Wata babbar kotun tarayya ta soki hukuncin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na gabatar da sunayen lauyoyi 11 gaban majalisa.

Buhari dai ya gabatar da sunayen lauyoyin ne domin majalisa ta tantance su da kuma tabbatar da su a matsayin alkalan babbar kotun tarayya, jaridar The Nation ta ruwaito.

A wani hukunci da ya yanke a ranar Laraba, Justis Ingang Ekwo ya riki cewa matakin da Shugaba Buhari ya dauka ya yi karo da sashi na 256(2) na kundin tsari lokacin da ya gabatar da sunayen da majalisar alkalai ta tura masa, zuwa gaban majalisar dattawa.

KU KARANTA KUMA: Obaseki: Ba ni da niyyar komawa APC, ina cikin PDP daram

Da duminsa: Kotu ta ƙalubalanci Buhari kan miƙa sunayen lauyoyi 11 don mayar da su masu shari'a
IDa duminsa: Kotu ta ƙalubalanci Buhari kan miƙa sunayen lauyoyi 11 don mayar da su masu shari'a Hoto: Nairametric/Thisday
Asali: UGC

Justis Ekwo ya ce a waje daya da aka yarda shugaban kasar yana iya gabatar da shawarar majalisar alkalai gaban majalisa, game da nadin alkalin babbar kotun tarayya, shine idan yana da nasaba da nadin shugaban kotu, kamar babbban alkali.

Sai dai kuma alkalin ya bayyana cewa duk da cewar Shugaba Buhari ya saba dokar sashi na 256(2) na kundin tsari, hakan ba zai shafi bikin rantsar da alkalan ba.

KU KARANTA KUMA: Idan aka bani dama: Ina da burin zama shugaban kasar Nigeria a 2023 - Okorocha

A wani labarin kuma, mun ji cewa an nada Farfesa Abba Isa Tijjani a matsayin sabon shugaban hukumar gidajen ajiye kayan tarihi ta kasa (NCMM).

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da nadin Tijjani a matsayin sabon shugaban NCMM, wanda ya daga darajar masanin ilimuka daga Malami zuwa Shugaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel