Garar N30 a Kano: Bayan shekara daya, gidan cin abincin ya kasa cigaba da aiki

Garar N30 a Kano: Bayan shekara daya, gidan cin abincin ya kasa cigaba da aiki

- A sakamakon tsadar kayan abinci a fadin kasar nan, gidan cin abincin N30 ya daina aiki a Kano

- Mai gidan abincin mai suna Haruna ya koka da yanayin tsadar da kayan abinci suka yi a jihar

- Ya yi kira ga shugaban kasa muhammadu Buhari da ya duba tare da kawo musu dauki

Sakamakon tsadar kayan abinci, an rufe sanannen wurin cin abincin nan na N30 da ke Kano, da ya kawo cece-kuce.

An bude wurin cin abincin shekarar da ta wuce, tun bayan wata hira da akayi da ministan noma, inda yace, "da N30 mutum zai iya kwasar girki a Kano".

Haruna Engineer ya yanke shawarar bude wurin cin abincin ne duk don ya bi bayan maganar ministan harkokin gona, Sabo Nanono, wanda yace "da kankanin kudinka kamar N30, zaka samu abincin ka mai rai da motsi a Kano."

Sakamakon haka, mutane suka yi ta tururuwar zuwa siyan abinci kamar shinkafa, wake da gari.

A makon da ya gabata, chronicle ta ziyarci wurin cin abincin Haruna da ke Layin Kuka, yankin Sani mai Nagge da ke birnin kano amma sai aka tarar da wurin a kulle.

A yayin zantawa da Daily Trust, haruna wanda tuni ya koma tsohon kasuwancinsa na gyaran kayan wuta, ya ce dole ce ta sa yarufe wurin cin abincinsa saboda tashin kayan abinci.

KU KARANTA: Matasa 3 sun saki bidiyon fyaden da suka yi wa budurwa ana gab da bikinta, ango ya fasa

"Ba zai yuwu in cigaba da aiki a wurin cin abincin ba saboda hawan farashin kayan abinci.

"Lamarin ya sauya saboda a yanzu gari ya koma N600 a maimakon N200, shinkafa N1,300 a maimakon N400 kuma kayan lambu sun tashi," yace.

"Ina kira ga shugaban kasa da ya duba halin da muke ciki, talakawa a yanzu da kyar suke cin abinci," ya kara da cewa.

Haruna yace lamarin ya yi kamari sakamakon kullen annobar korona wanda yasa komai ya sake wahala.

Haruna yace, ya dauka mata 11 da ke masa girki da wasu biyar da ke siyar da abincin amma duk yanzu ya sallamesu.

Garar N30 a Kano: Bayan shekara daya, gidan cin abincin ya kasa cigaba da aiki
Garar N30 a Kano: Bayan shekara daya, gidan cin abincin ya kasa cigaba da aiki. Hoto daga FMA
Source: Getty Images

KU KARANTA: Gwamnatin Katsina ta musanta bai wa tubabbun 'yan bindiga gidaje da shaguna

A wani labari na daban, Kotun shari'ar Musulunci ta jihar kano ta yanke wa Shariff-Aminu dan shekara 22 hukuncin kisa bayan an kama shi dumu-dumu da laifin batanci ga manzon Allah, a wata wakarsa da ta yi ta yawo a kafar sada zumuntar zamani ta WhatsApp.

Alkali Aliyu Muhammad Kani yace wanda ake zargin zai iya daukaka kara matukar bai gamus da hukunci da aka yanke masa ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel