Katsina: Buhunan hatsi su na yin sauki bayan shigowar amfanin gona
- Rahotanni sun ce farashin kayan abinci sun fara sauka a kasuwanni
- A yankin Kaduna da Katsina, hatsi sun rage tsada a kwanakin nan
- Hakan na zuwa ne bayan an fara cire kayan amfanin noman damina
Rahotanni daga jaridar Katsina Post sun bayyana cewa kayan abinci sun fara rage kudi a halin yanzu.
Masu saida hatsi da dillalai sun tabbatar da cewa buhunan kayan gona su na rage kudi a wasu manyan kasuwannin hatsi da ake da su.
Ana zargin hakan bai rasa alaka da sababbin hatsin da su ka fara shigowa a sakamakon girbe kayan amfanin gona da manoma su ka fara yi.
‘Yan jaridar sun tabbatar da cewa abinci sun rage kudi a halin yanzu, bayan sun kai ziyara zuwa kasuwannin Babbar Ruga da ta ‘Yar kutungu.
KU KARANTA: Ba za a dade ana fama da tsadar kayan abinci ba - Hadimin Buhari
Ana yin cinikin hatsi a wadannan kasuwanni da ke cikin karamar hukumar Batagarawa da Katsina.
Jaridar ta bayyana cewa a kasuwar Babbar Ruga, buhun gero ya tashi ne a kan N14, 000, akasin N26, 000 da aka saida shi a makon da ya gabata.
Haka zalika buhun masara ya rage kudi a yanzu, daga N23, 000 an koma saida buhu a kan N20, 000.
A wadannan kasuwanni, ana saida sabuwar masara wacce ta shigo gari a kimanin N14, 000.
KU KARANTA: Abin da ya jawo mana tsadar abinci - Buhari
Mudun gero ya koma N400 maimakon N500 da aka rika saida shi a kasuwar ‘Yan kutungu kwanakin baya, an samu raguwar kusan 30% a farashi.
A kasuwar Saminaka ma dai hatsi sun rage tsada, sabuwar masara ta karye. Haka zalika farashin babban buhun shinkafa ya fadi war-was a makon jiya.
A kwanan baya aka ji Hadimin shugaban kasa, Garba Shehu ya na cewa farashin hatsi ya na sauka a Najeriya bayan mugun tsadar da su ka yi a watan nan.
Shehu ya yi wannan jawabin ne a dalilin kukan da ‘yan kasa su ke yi na tsadar halin rayuwa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng