Zulum ya bawa iyalin marigayi Kanal Bako kyautar gida da N20m (Hotuna)

Zulum ya bawa iyalin marigayi Kanal Bako kyautar gida da N20m (Hotuna)

- A ranar Litinin ne rundunar soji ta fitar da sanarwar mutuwar kwamanda a rundunar atisayen LAFIYA DOLE, Kanal DC Bako

- Kanal Bako ya rasu a wani asibiti bayan an yi ma sa tiyata sakamakon samun munanan raunuka yayin da mayakan Boko Haram su ka kaiwa tawagarsa hari

- A ranar Talata aka binne gawar Kanal Bako a makabartar sojoji ta Maimalari da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da bawa mata da 'ya'yan marigayi Kanal Dahiru Chiroma Bako kyautar gida da kudi Naira miliyan ashirin (N20m).

Farfesa Zulum ya sanar da hakan ne ranar Talata yayin jana'izar marigayi Kanal Bako wacce aka yi a makabartar sojoji ta Maimalari da ke Maiduguri jihar Borno.

Yayin da ya ke gabatar da jawabi a wurin jana'izar, Farfesa Zulum ya ce; "Kanal Bako jarumin soja ne marar tsoro, saboda kokarinsa ne har yanzu mayakan Boko Haram su ka gaza cimma Damboa.

"Ya na da kwazo da himma wajen aikinsa, ba rundunar soji ce kadai ta yi rashi ba, jihar Borno da Najeriya sun yi babban rashin gwarzon da ya bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen kassara kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

"Ba zamu taba mantawa da irin kokarinsa ba, Allah ne kadai zai yi masa sakayya, Allah ya gafarta masa.

Zulum ya bawa iyalin marigayi Kanal Bako kyautar gida da N20m (Hotuna)
Matar Marigayi kanal Bako da Janar Buratai a wurin jana'iza
Source: Facebook

"Na ji an ce Kanal Bako bashi da gidan kansa kafin ya rasu, a saboda haka gwamnatin jihar Borno ta dauki nauyin ginawa iyalinsa gida. Kanal Bako bai mutu a banza ba, a saboda haka ba zamu manta da iyalinsa ba.

"Domin walwalar iyalinsa, gwamnatin jihar Borno ta amince da bawa iyalinsa tallafin miliyan N20, takardar fitar da kudin daga banki za ta shiga hannun matarsa a yau da yamma ko gobe da safe," cewar Zulum.

A ranar Litinin ne rundunar soji ta Najeriya ta sanar da mutuwar Kanal D. C. Bako, kwamandar runduna ta 25, wanda mayakan kungiyar Boko Haram su ka kashe a jihar Borno.

Ado Isa, kakakin rundunar atisayen Lafiya Dole, ya ce Kanal Bako ya mutu ne sakamakon raunukan da ya samu bayan mayakan kungiyar Boko Haram sun kai wa tawagarsa harin kwanton bauna yayin da suka fita sintiri.

KARANTA: Ma'aikaci a jihar Jigawa ya rasu tare da 'ya'yansa da matarsa a hatsarin mota a hanyar Gaya-Dutse

A cikin jawabin da Isa ya fitar ranar Litinin, ya ce Kanal Bako ya rasu a asibitin sojoji duk da ya fara nuna alamun farfadowa bayan an yi masa tiyata.

"Rundunar atisayen Lafiya Dole ta rasa jarumi, daya daga gwarazanta na yaki, Kanal DC Bako.

"A matsayinsa na kwamanda, kullum shine a gaba idan rundunarsa za ta fita aiki.

"Da irin wannan salon jarumta ne ya jagoranci rundunarsa zuwa yankin Sabon Gari - Wajiroko a Damboa domin kawar da sauran mayakan kungiyar Boko Haram a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba.

"Dakarun soji, a karkashin jagorancinsa, sun samu nasarar dakile harin kwanton baunar da aka kai mu su tare da samun nasarar kwace makaman 'yan ta'adda.

KARANTA: Babu sauran APC, abu daya ke rike da jam'iyyar - Sanata Rochas Okorocha

"Sai dai, abin takaicin shine Kanal Bako ya samu munanan raunuka kasancewar shine a gaba yayin da sojoji ke yin musayar wuta da 'yan ta'addar da suka kai musu harin kwanton bauna da misalin karfe 10:00 na safe.

"Kanal Bako ya fara farfadowa a asibiti bayan an yi masa tiyata, har ya samu damar yin Sallah da safiyar yau, Litinin, kafin ya rasu a asibiti.

"Mu na addu'a Allah ya ji kansa," a cewar sanarwar da Isa ya fitar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel