Budurwar da mahaifiyarta za ta mutu ta shirya aurenta cikin kwana 5, an daura aurenta a cikin asibiti
- Amaryar tace tasan yakamata tayi wani abu tun bayan da likita yace saura makonni kadan mahaifiyarta ta bar duniya
- Mahaifiyar Linda mai shekaru 71 da haihuwa tana fama da cutar sankarar hunhu, tsawon shekaru 2 anata kokarin magani amma abu ya gagara
- bayan ta rantse akan bazata taba yin aure ba kwatsam sai ga saurayinta ya hada kwarya-kwaryan shagalin aurensu cikin kwanaki 5
Wata amarya da ta rantse bazata yi aure ba saboda mahaifiyar ta tana fama da matsanancin ciwo ta shirya yin aure cikin kwanaki 5.
Mahaifiyar Nicole Linda, Elizabeth Bridgewater mai shekaru 71 da haihuwa ta sha mamaki matuka sakamakon ganin dakinta na asibiti cike da mutane, kowa yaci ado irin na biki har da masu neman auren diyar ta a ciki.
Mahaifiyar Linda Bridgewater ta kalli diyar ta cikin mamaki akan abinda ke faruwa, tsananin murna ya sanya ta zubar da hawayen shauki yayinda ta gane ba mafarki takeyi ba.
An jiyo muryar mahaifiyar tana kuka a wani bidiyo da 'yar uwar Linda ta dauka.
An dauki hotunan a asibitin Queen Elizabeth University, Glasgow, inda mahaifiyar Linda take kwance tana jinya.
KU KARANTA: Matar da ta aike wa Trump wasika mai guba ta shiga hannun jami'an tsaro
Amaryar da Angon nata sunyi aure ne a asibitin da mahaifiyar ta take kwance tana jinya.
Mutane kadanne suka halarci daurin auren saboda cutar coronavirus.
Linda tayi hanzarin yin auren ne saboda jin mummunan labarin cewa saura makonni kadan mahaifiyarta ta rasu bayan shekaru 2 tana jinya.
Mahaifiyarta ta fashe da kuka tana cewa a tunaninta bazata taba ganin auren diyar ta ba.
"Nasan ya kamata inyi wani abu akan hakan," cewar angon. "Nayima James magana akai ranar Monday, take anan ya amince akan aurenmu ranar Asabar," a cewar Amaryar.
KU KARANTA: Yadda aka kama dan shekara 16 da bindiga a makarantar sakandare
An dakatar da daurin auren wasu masoya a Jihar River, bayan wani mutumi ya fito ya bayyana cewa shine mahaifin amaryar da angon, a yayin da ake shirin daura auren.
Anne Magwi da Jotham Munini, wadanda ya kamata a daura aurensu a ranar Asabar, 5 ga watan Satumba, an ruwaito cewa iyayensu daya.
Sai dai kuma a wani rahoto da jaridar The Nation ta ruwaito, ya nuna yadda mahaifinsu tare da 'yan uwanshi suka isa wajen daurin auren, suka dakatar da daurin auren.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng