Zaben Edo: Jama'ar Edo sun bai wa masu magudin zabe kunya - Kwankwaso

Zaben Edo: Jama'ar Edo sun bai wa masu magudin zabe kunya - Kwankwaso

- Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Kwankwaso yayi magana game da nasarar da suka samu a zaben gwamnan jihar Edo

- A cewar Kwankwaso, mutanen jihar ba kada kuri'a kadai sukayi ba,sai da suka tsaya suka sa'ido sannan suka raka akwatunansu

- Tsohon sanatan ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter inda yake taya Gwamna Obaseki da jama'ar jihar Edo murna

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wallafar taya murnar nasara da suka samu a yayin zaben jihar Edo a shafinsa na Twitter.

Yana cewa, "Mutanen kirkin jihar Edo sunyi magana. Mutane sun nuna zabinsu na gaskiya. Don haka, inaso inyi amfani da wannan damar domin taya mutanen jihar Edo murnar gama zaben gwamnoni lafiya, kuma cikin kwanciyar hankali."

Ya kara da cewa, "Inaso in taya mutanen jihar Edo murna musamman saboda tsayuwa da dagewa wurin kara zabar jagora mai dagewa wurin yin aiki tukuru, don ya cigaba da ciyar da jihar Edo gaba.

"Ina taya mai girma Gwamna Obaseki murna akan nasarar da ya samu, duk da dama ya cancanta. Yayi aiki tukuru ga mutanen jihar Edo, kuma sun nuna godiyarsu wurin kada maka kuri'u masu yawa.

"Sun kara da tsayuwa tsayin-daka saboda tabbatar da yan magudin siyasa da suka zo daga bangarori daban-daban basu samu nasara ba.

"Wannan zai kara bai wa duk wani dan Najeriya kaimi. Babu shakka, shugaban kungiyar kamfen na PDP, mai girma Nyesom Wike na jihar Ribas da duk wasu yan kungiya sunyi kokari matuka, kuma sun jajirce kwarai wurin ganin nasarar nan ta tabbata."

Kwankwaso yayi godiya ga yan jam'iyyar PDP na jihar, yana nuna farin cikinsa kwarai sakamakon nasarar da PDP ta samu a jihar Edo, Vanguard ta wallafa.

KU KARANTA: Hotuna: Dubban mazauna Edo sun sha shagali bayan Obaseki ya fito murna a tituna

Zaben Edo: Jama'ar Edo sun bai wa masu magudin zabe kunya - Kwankwaso
Zaben Edo: Jama'ar Edo sun bai wa masu magudin zabe kunya - Kwankwaso. Hoto daga Vanguard
Source: Twitter

KU KARANTA: Zaben Edo: Buhari bai taba amfani da karfin ikonsa wurin magudi ba - El-Rufai

A wani labari na daban, Gwamna Obaseki ya aika da sako mai matukar muhimmanci ga dan takarar jam'iyyar APC, Osagie Ize-Iyamu, bayan lallasa shi da yayi a zaben da ya gabata.

Gwamnan ya yi kira garesa da ya rungumi zaman lafiya tare da dawowa wurinsa domin kawo cigaba ga jihar baki daya.

A yayin tattaunawar da yayi da BBC a ranar Lahadi, 20 ga watan satumba, bayan bayyana shi a matsayin wanda yayi nasarar lashe zaben, Obaseki ya sanar da Ize-Iyamu cewa jama'a sun riga sun bayyana zabinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel