Babu sauran APC, abu daya ke rike da jam'iyyar - Sanata Rochas Okorocha
- Jam'iyyar APC ta sha kaye a hannun jam'iyyar PDP a zaben kujerar gwamnan jihar Edo da aka kammala ranar Asabar
- Yanzu haka jam'iyyar APC ba ta da kujerar gwamna ko daya a yankin kudu maso kudancin Najeriya
- Da kyar da 'yan dabaru APC ta samu kujerar gwamna a yankin kudu maso gabas na 'yan kabilar Igbo
Tsohon gwamna kuma Sanata mai ci a yanzu, Rochas Okorocha, ya ce girma da kimar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ne kawai ke rike da jam'iyyar APC a halin yanzu.
Sanata Rochas, jigo a APC, ya ce komai zai iya lalacewa a jam'iyyar matukar shugabanninta basu gaggauta daukan matakan gyara ba.
"Babu sauran APC, abinda Kawai ya rage shine mutunci da kimar shugaba Buhari, shine abinda ke rike da mu har yanzu.
"Mutuncinsa ne kawai ya ke rike damu, amma har yanzu za a iya gyarawa.
KARANTA: Mun gaji da zama a Arewa, za mu koma inda muka fito - Yarabawa
"Za mu iya cewa babu jam'iyyar APC a yankin kudu maso gabas. Da kyar da kuma 'yan dabaru mu ka samu jiha daya kacal, hakan ba abin alfahari bane," a cewar Rochas yayin da ya ke ganawa da manema labarai gabanin cikarsa shekaru 58 a duniya.
"Tun farko an samu sunan jam'iyyar APC ne daga jam'iyyun da suka yi maja a 2015 kafin daga bisani wasu mambobin PDP su shigo cikinta.
"Nine na kirkiri hatimi da taken jam'iyyar APC, a lokacin kawunanmu a hade suke, komai yana tagiya daidai.
"Amma yanzu komai ya sukurkuce, babu wani abu da ke rike da mu bayan girma da mutincin shugaba Buhari.
"Jama'a sun fara kosawa, ina ganin zaben 2023 zai zo da sabon salo don jama'a sun fara gane cewa mutum ne mai muhimmanci ba jam'iyyar da yake takara ba," a cewar Sanata Rochas.
KARANTA: Ma'aikaci a jihar Jigawa ya rasu tare da 'ya'yansa da matarsa a hatsarin mota a tsakanin Gaya zuwa Dutse
Legit.ng ta wallafa labarin cewa shugaban kasa Muhamadu Buhari ya taya Godwin Obaseki da jam'iyyar PDP murnar sake lashe zaben gwamnan jihar Edo, da aka gudanar ranar Asabar 20 ga watan Satumba, 2020.
A ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba, Hukumar zabe INEC ta sanar da Godwin Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan samun kuri'u 307,955.
Sai dai, wasu gwamnonin jam'iyyar APC sun ziyarci shugaba Buhari a fadarsa ranar Litinin a wani salo da wasu ke ganin ya na da nasaba da kayen da APC ta sha a zaben Edo.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng