Tsoro ya cika zukatan al’umman Ondo yayinda aka kama yan daba a motar kamfen din Jegede, APC ta yi martani

Tsoro ya cika zukatan al’umman Ondo yayinda aka kama yan daba a motar kamfen din Jegede, APC ta yi martani

- An shiga halin fargaba a Ondo gabannin zaben gwamnan jihar wanda za a yi a ranar 10 ga watan Oktoba

- An kama yan daba da makamai iri-iri a cikin wata motar Toyota Sienna mai dauke da hotunan kamfen din Jegede

- A yanzu lamarin ya haddasa cece-kuce tsakanin Gwamna Rotimi Akeredolu da Eyitayo Jegede (SAN)

Ana saura kasa da wata guda kafin zaben zaben Ondo, sabon rikici ya kaure tsakanin jam’iyyun Peoples Democratic Party (PDP) da All Progressives Congress (APC), kan kama wasu yan daba da aka yi wadanda ake zargin suna yi wa Eyitayo Jegede.

An kama yan iskan wadanda a Ifon da ke karamar hukumar Ose cikin wata mota dauke hotunan dan takarar PDP tare da makamai iri-iri, jaridar ThisDay ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Okorocha ya caccaki APC bayan PDP da Obaseki sun lashe zabe a Edo

Tsoro ya cika zukatan al’umman Ondo yayinda aka kama yan daba a motar kamfen din Jegede, APC ta yi martani
Tsoro ya cika zukatan al’umman Ondo yayinda aka kama yan daba a motar kamfen din Jegede, APC ta yi martani Hoto: Thisday
Source: UGC

An tattaro cewa yan daban na a cikin wata mota kirar Toyota Sienna wacce akan kawata da hotunan kamfen din Jegede lokacin da dubunsu ta cika a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba.

Sai dai Jegede da PDP sun nesanta kansu daga yan daban, wanda hakan ya haifar da sabon cece-kuce tsakanin tsohon atoni janar na Ondo da gwamna mai ci, Oluwarotimi.

Za a gudanar da zaben gwamnan Ondo a ranar 10 ga watan Oktoba, 2020.

Da yake martani ga kamun yan daban, Gwamna Akeredolu ta kakakin kungiyar kamfen dinsa, Olatunde Richard, ya nuna dimuwa.

Sannan ya zargi jam’iyyar adawa da kokarin cin mambobin APC da yaki.

Muna mamakin ko PDP na kallon zaben a matsayin wani yaki ne ko takarar kujerar gwamnan jiha,” in ji Richard.

Sai dai PDP ta bayyana kama yan daban a matsayin “wani yunkuri da APC ke yi na cimma mugun nufinta.”

KU KARANTA KUMA: Buhari ya yi ganawar sirri da takwaransa na Ghana a Abuja

A baya mun ji cewa, an yi wata arangama a tsakanin magoya bayan dan takarar jam'iyyar PDP, Eyitayo Jegede, da wasu magoya bayan jam'iyyar APC a garin Oba Akoko da ke karamar hukumar Akoko ta kudu ma so yamma a jihar Ondo.

Bayan aragamar ne Jegede ya yi korafin cewa an tayar da hargitsin ne tun farko saboda ana neman rayuwarsa.

Jegede ya bayyana cewa an lalata motoci 15 daga cikin motocin da ke cikin tawagarsa tare da raunata wasu daga cikin magoya bayansa.

Ya bayyana cewa an yi hakan ne domin kassara yakin neman zabensa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel